Malam Ibrahim Shekarau ya sayi takardan takara kujeran Sanatan mazabar da Kwankwaso ke wakilta

Malam Ibrahim Shekarau ya sayi takardan takara kujeran Sanatan mazabar da Kwankwaso ke wakilta

Tsohon gwamnan jihar Kano, Mallam Ibrahim Shekarau, ya sayi takardan takara kujeran Sanata mai wakiltan mazabar Kano ta tsakiya karkashin jam'iyyar All Progressives Congress a yau Talata, 11 ga watan Satumba, 2018.

Malam Shekarau ya maye gurbin Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, da ke takaran kujeran shugaban kasa a jam'iyyar PDP.

Shekarau ya koma jam'iyyar APC bayan rikicin da ya barke tsakaninsa na Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.

Malam Ibrahim Shekarau ya sayi takardan takara kujeran Sanatan mazabar da Kwankwaso ke wakilta
Malam Ibrahim Shekarau ya sayi takardan takara kujeran Sanatan mazabar da Kwankwaso ke wakilta
Asali: Facebook

Rikici ya barke ne musamman tsakanin Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso da wasu manyan jigogin jam’iyyar PDP a jihar wadanda suka kunsho tsohon gwamnan jihar Malam Ibrahim Shekarau, Ambasada Aminu Wali, Sanata Bello Hayatu Gwarzo da sauran su.

KU KARANTA: Yan Najeriya sun aminta da riƙon amanar mu - INEC ga PDP

Wata daya bayan sauya shekan Sanatan Rabi’u Musa Kwankwaso zuwa jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) daga All Progressives Congress (APC), rikici ya kunno kai cikin sashen jam’iyyar PDP a jihar Kano.

Wannan rikici ya fara ne a lokacin da jam’iyyar PDP ta kasa ta sauke dukkan shugabannin jam’iyyar a jihar da kuma nada sabbin wadanda za su jagoranci mambobin jam’iyyar.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel