Direbobin Keke Napep sun bankawa ofishin VIO wuta a Abuja

Direbobin Keke Napep sun bankawa ofishin VIO wuta a Abuja

- Rashin jituwa tsakanin direbobin Keke Napep da VIO ya janyo direbobin sun kona ofishin VIO da ke Abuja

- Wasu direbobin VIO sunce an kone ofishin ne saboda jami'an VIO sun lalata musu Keke Napep sama 50

- Mai magana da yawun VIO ya ce masu Keke Napep din suna ayyuka a unguwanin da aka haramta musu shiga

Mun samu daga Premium Times cewa wasu da ake kyautata zaton masu Keke Napep (adaidaita-sahu) ne sun kona ofishin Jami'an Kula da ababen hawa (VIO) da ke Idu a babban birnin tarayya, Abuja.

Makwabta da Jami'an VIO sun ce an bankawa ofishin wuta ne a daren Alhamis a wani hari da ake kyautata zaton ramuwar gayya ce saboda jami'an hukumar sunyi kame inda suka fasa gilashen adaidaita sahu sama da 50 a ranar Ahamsis.

Wutar da aka bankawa ofishin da ke unguwar Idu kusa da Life Camp ya yi sanadiyyar konewar Generator, kayan aiki, tabura, kujeru, lambar ababen hawa, takardu masu dauke da bayyanai masu muhimmanci da sauran kayayaki.

Direbobin Keke Napep sun bankawa ofishin VIO wuta a Abuja
Direbobin Keke Napep sun bankawa ofishin VIO wuta a Abuja
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Raba kafa: 'Yan takarar PDP 3 sun sayi fam din takara 2

Majiyar Legit.ng ta ruwaito yadda masu adaidaita sahun su kayi zanga-zanga inda suka janyo cinkosa a wasu sassan birnin tarayya Abuja.

Babu wani jami'in kungiyar masu adaidaita-sahu da ya amsa cewa su suka kone ofishin amma wasu direbobin sum amsa cewa 'yan kungiyar ne suka kone ofishin.

"Jami'an VIO sun lalata Keke Napep masu dimbin yawa a ranar Alhamis, hakan yasa direbobin Keke Napep suka kona ofishinsu," inji wani direban Keke Napep da ke kusa da Life Camp Junction.

"Sun saba karbar kudade a hannun mu, kullum sai mun biya N400 kudin tikiti kuma bayan hakan sukan karba kudi a hannun mu duk lokacin da suka tare mu. Jiya ma sun karbi N12,000 daga hannu na. Abinda yasa ran mu ya baci kenan," inji wani direban.

Kakakin VIO ya ya bayannin cewa jami'an sun lalata Keke Naped da yawa ne saboda direbobin na zuwa unguwannin da ba'a amince su shiga ba kuma sunki amincewa a hukuncin da jami'an hukumar ta zartas a kansu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel