Gwamnatin Kano ta bayyana ranar hutun sabuwar shekarar Musulunci

Gwamnatin Kano ta bayyana ranar hutun sabuwar shekarar Musulunci

Gwamnatin jihar Kano ta bayyana gobe, Talata, 11 ga watan Satumba, a matsayin ranar hutu domin murnar shiga sabuwar shekarar Musulunci, 1440 bayan Hijra.

Wannan sanarwa na kunshe ne cikin wata takardar da kwamishinan yada labarai na jihar kano, Malam Muhammad Garba, ya saka hannu a kan ta kuma aka raba ga manema labarai a yau, Litinin.

Gwamnan jihar Kano, Dakta abdullahi Umar Ganduje, ya taya musulmi murnar zagayowar sabuwar shekarar Musulunci wacce ke farawa a watan Muharram, watan farko a jerin watannin Islama.

Gwamnatin Kano ta bayyana ranar hutun sabuwar shekarar Musulunci
Gwamnan Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje.
Asali: Depositphotos

Ganduje ya bukaci Musulmi da su kasance masu koyi da biyayya ga aiyuka masu kyau da addinin Musulunci ya zo da su tare da yin addu’ar neman zaman lafiya da cigaban kasa.

Kazalika ya jaddada niyyar gwamnatinsa na cigaba da aiyukan raya kasa da inganta rayuwar jama’ar jihar ta Kano.

DUBA WANNAN: El-Rufa'i ya halarci bikin bude makarantar islamiyya da jigo a PDP ya gina a Zaria

Kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) ya rawaito cewar ranar Talata ce zata kasance rana ta farko a sabuwar shekarar Musulunci.

A wani lamari da ya kara jan hankali a fagen siyasar shine yadda gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya zagayi garin Kano ba tare da jar hula a kansa ba.

Dama gwamna Ganduje ya dade da cin al washin daina saka jar hula bayan dangantaka tsakaninsa da tsohon gwamna Kwankwaso ta lalace.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel