Gwamnan Kaduna ya bayyana yadda ya fara rayuwar sa yana Maraya

Gwamnan Kaduna ya bayyana yadda ya fara rayuwar sa yana Maraya

Mun samu labari cewa Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufai ya bayyana yadda ya fara rayuwar sa lokacin yana Maraya har ta kai ya samu ilmi ya zama abin da ya zama a cikin Duniya.

Gwamnan Kaduna ya bayyana yadda ya fara rayuwar sa yana Maraya
Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufai a ofis
Asali: UGC

Kwanan nan ne aka yi wani taro kan adabi da aka saba shiryawa a Jihar Kaduna tun da Nasir El-Rufai ya zama Gwamna inda ake sharhin litattafai da rubutattun wake da dai sauran su domin canza tunanin Jama’a da bunkasa adabi.

Wannan karo kamar yadda mu ka samu labari Gwamna El-Rufai ya bayyana cewa ya fara rayuwar sa ne a Kauyen Daudawa a cikin Kudancin Jihar Katsina. Gwamnan yace yana karamin yaro ‘Dan shekara 8 ya zama Maraya a Duniya.

Malam Nasir El-Rufai ya kuma bayyana cewa ko dama can Mahaifin sa tsohon Ma’aikacin Gwamnati ne wanda yake karbar fansho kafin ya bar Duniya. Gwamnan yace sai dai duk da haka a wancan lokaci ya samu ilmi mai nagarta.

KU KARANTA: An fasa kara albashin masu bautar kasa a Najeriya

Nasir El-Rufai yace ko da Makarantar Gwamnati yayi, ya samu karatu daidai gwargwado har ta kai ya zama yayi karatun Jami’a ya zama shugaba a Gwamnati. A lokacin mulkin Obasanjo ne aka nada el-Rufai a matsayin Ministan Abuja.

Gwamnan na Kaduna dai ya saba bayyana cewa wannan yana cikin dalilin da ya sa yake kokarin gyara harkar ilmi domin ‘Dan talaka ya zama wani a kasar nan nan gaba kamar yadda ya zama. Tuni dai Gwamnan ya dauki matakan gyara ilmi a Jihar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel