Bikin manya: Shugabannin Najeriya sun halarci bikin diyar Ministan Buhari, hotuna

Bikin manya: Shugabannin Najeriya sun halarci bikin diyar Ministan Buhari, hotuna

- Mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, ya halarci bikin Zakiyya, diyar ministan shari’a, Abubakar Malami

- An yi bikin Zakiyya da angonta, Saifullahi Gishiri, a garin Birnin Kebbi na jihar Kebbi ranar Asabar

- Gwamnoni da manyan masu rike da mukamai a gwamnatin shugaba Buhari sun halarci bikin

A ranar Asabar ne garin Birnin Kebbi na jihar Kebbi ya cika da manyan baki daga fadin Najeriya domin halartar daurin auren diyar ministan shari’a na kasa, Abubakar Malami.

Bikin manya: Shugabannin Najeriya sun halarci bikin diyar Ministan Buhari, hotuna
Shugabannin Najeriya sun halarci bikin diyar Ministan Shari'a
Asali: Facebook

Bikin manya: Shugabannin Najeriya sun halarci bikin diyar Ministan Buhari, hotuna
Shugabannin Najeriya sun halarci bikin diyar Ministan Buhari
Asali: Facebook

An daura auren na Zakiyya Abubakar Malami da Saifullahi Gishiri a fadar sarkin Gwandu, Alhaji Muhammadu Bashar.

DUBA WANNAN: 2019: 'Yan takarar PDP 6 da zargin cin hanci ya yiwa dabaibayi

Mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo, ya samu tarbar girma yayin da ya isa garin Birnin Kebbi domin halartar daurin auren.

Gwamnonin jihohin Kaduna, Katsina, Jigawa, Zamfara, Sokoto da kuma mai masaukin baki gwamnan jihar Kebbi sun halarci wurin daurin auren.

Bikin manya: Shugabannin Najeriya sun halarci bikin diyar Ministan Buhari, hotuna
Shugabannin Najeriya sun halarci bikin diyar Ministan Buhari
Asali: Facebook

Bikin manya: Shugabannin Najeriya sun halarci bikin diyar Ministan Buhari, hotuna
Shugabannin Najeriya sun halarci bikin diyar Ministan Buhari
Asali: Twitter

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel