Kurunkus: Shekarau ya yanki katin APC, Ganduje ya rabu da jar hula (Hotuna)
- A jiya, Asabar, ne shekarau ya gana da dubban magoya bayansa a jihar Kano domin shaida masu dalilinsa na ficewa daga jam’iyyar PDP
- Shekararau ya yanki katin shaidar zama dan APC a ofishin jam'iyyar dake mazabar sa, Giginyu, a karamar hukumar Nasarawa
- Ana hasashen cewar jam’iyyar APC tayi alkawarin tsayar da Shekarau ya maye gurbin kujearar Sanatan Kano ta tsakiya, Rabi’u Musa Kwankwaso
Tsohon gwamnan jihar Kano, Malam Ibrahim Shekarau,ya bayyana cewar rashin adalcin da uwar jam’iyyar PDP ta nuna masa ne silar komawarsa jam’iyyar APC. Shekarau ya bayyana hakan ne yayin gabatar da jawabi ga dubban magoya bayansa daga kananan hukumomin Kano 44 a wurin gangamin taron bikin karbarsa a jam’iyyar APC da aka yi a gidansa dake unguwar Mundubawa.
A karshe, Malam Ibrahim Shekarau, ya yanki katin shaidar zama dan APC a ofishin jam'iyyar dake mazabar sa ta Giginyu a karamar hukumar Nasara dake Kano a yau, Lahadi.

Asali: Twitter

Asali: Twitter
Shekarau ya ce ya bar PDP ne saboda shawarar da uwar jam’iyyar ta yanke na mika kashi 51% na shugabancinta a jihar Kano ga dan sanatan kano ta tsakiya kuma dan takarar shugaban kasa, Rabi’u Musa Kwankwaso. Ana hasashen cewar jam’iyyar APC tayi alkawarin tsayar da Shekarau yam aye gurbin kujearar Sanatan Kano ta tsakiya, Rabi’u Musa Kwankwaso.
DUBA WANNAN: Arziki: Tarihin attajirin Najeriya da ke aika wanki da gugar kayansa kasar Ingila
A wani lamari da ya kara jan hankali a fagen siyasar shine yadda gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya zagayi garin Kano ba tare da jar hula a kansa ba.
Dama gwamna Ganduje ya dade da cin al washin daina saka jar hula bayan dangantaka tsakaninsa da tsohon gwamna Kwankwaso ta lalace.

Asali: Twitter

Asali: Twitter
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng