'Yan Takara 12 dake neman Kujerar shugaban kasa, 120 sun mallaki fam din Kujerun Gwamna a jam'iyyar PDP

'Yan Takara 12 dake neman Kujerar shugaban kasa, 120 sun mallaki fam din Kujerun Gwamna a jam'iyyar PDP

Mun samu cewa akwai 'yan siyasa 120 da kowanen su ya biya N6m domin mallakar fam na takarar kujerun gwamna a fadin kasar nan karkashin inuwa ta jam'iyyar PDP kamar yadda binciken jaridar The Punch a karshen makon nan ya bayyana.

Kazalika jam'iyyar ta sayar da fam din bayyana kudirin takarar kujerar shugaban kasa ga 'yan siyasa 12 inda kowanen su ya biya N12m ga jam'iyyar domin mallaka da hankoron tikitin ta na takara.

Sai dai binciken manema labarai bai iya tantance jerin 'yan takarar kujerun gwamnan daki-daki ba na kowace jiha, inda ba bu shakka kowace jiha na da samfurin 'yan takarar ta da za su fafata salon siyasa daban-daban.

Rahotanni sun bayyana cewa, akwai misalin jihar Kwara inda akwai 'yan takara 6 na jam'iyyar PDP dake hankoron kujerar gwamnatin jihar.

Yayin da 'Yan Takara 12 ke neman Kujerar shugaban kasa, 120 sun mallaki fam din Kujerun Gwamna a jam'iyyar PDP
Yayin da 'Yan Takara 12 ke neman Kujerar shugaban kasa, 120 sun mallaki fam din Kujerun Gwamna a jam'iyyar PDP
Asali: UGC

Wasu daga cikin 'yan takarar na jihar Kwara sun hadar da; Tsohon kakakin jam'iyyar APC na kasa kuma tsohon Ministan wasanni, Mallam Bolaji Abdullahi, wani dan majalisar wakilai; Zakari Muhammad, tsohon ministan tsare-tsaren kasa; Farfesa Abubakar Suleiman.

'Yan Takara 12 dake neman Kujerar shugaban kasa, 120 sun mallaki fam din Kujerun Gwamna a jam'iyyar PDP
'Yan Takara 12 dake neman Kujerar shugaban kasa, 120 sun mallaki fam din Kujerun Gwamna a jam'iyyar PDP
Asali: Depositphotos

Sauran masu hankoron kujerar gwamnatin jihar sun hadar da; wani tsohon jami'in dan sanda; Mista Ibrahim Ajia da kuma wasu mutane 2 na hannun daman shugaban majalisar dattawa; Abubakar Bukola Saraki.

A yayin da adadin 'yan takara na kowace jiha suka bambanta, binciken manema labarai ya tabbatar da cewa jam'iyyar ta na dan takara guda daya tilo a jihar Oyo, Mista Seyi Makinde.

KARANTA KUMA: Cikin Hotuna: Ministan Shari'a, Abubakar Malami, ya aurar da diyarsa a Jihar Kebbi

Legit.ng ta kawo mu ku jerin 'yan siyasa da suka mallaki fam din takarar kujerar shugaban kasa na jam'iyyar da suka hadar da; Shugaban majalisar dattawa; Abubakar Bukola Saraki, Gwamnan jihar Sakkwato; Aminu Tambuwal, Gwamnan jihar Gombe; Ibrahim Dankwambo da kuma tsohon shugaban majalisar dattawa; David Mark.

Cikin jeranton akwai kuma tsohon gwamnan jihar Filato; Sanata Jonah Jang, tsohon gwamnan jihar Kaduna; Sanata Ahmed Makarfi, tsohon gwamnan jihar Kano; Sanata Rabi'u Kwankwaso, tsohon gwamnan jihar Jigawa; Alhaji Sule Lamido, tsohon gwamnan jihar Sakkwato; Attahitu Bafarawa, Dakta Datti Baba-Ahmed da kuma tsohon Ministan ayyukan na musamman; Alhaji Tanimu Turaki.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel