Oshiomhole ya yabawa Shekarau kan sauya sheka zuwa jam'iyyar APC

Oshiomhole ya yabawa Shekarau kan sauya sheka zuwa jam'iyyar APC

A ranar Juma'ar da ta gabata ne shugaban jam'iyyar APC na kasa, Kwamared Adams Oshiomhole, ya yiwa tsohon gwamnan jihar Kano, Mallam Ibrahim Shekarau, lale maraba gami yaba masa dangane da sauyin sheka zuwa jam'iyyar.

Shekarau wanda tsohon Ministan Ilimi ne a karkashin tsohuwar gwamnatin Najeriya ta Goodluck Jonathan, ya tabbatar da sauyin shekarsa daga jam'iyyar adawa ta PDP zuwa APC a ranar yau ta Asabar.

Legit.ng ta ruwaito cewa, a ranar da ta gabata ne shugaban jam'iyyar da tare da gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, suka ziyarci tsohon gwamnan a gidansa na Unguwar Mundubawa dake birnin Kano domin zawarci gami rinjayarsa akan dawowa jam'iyyar ta APC.

Oshiomhole ya yabawa Shekarau kan sauya sheka zuwa jam'iyyar APC
Oshiomhole ya yabawa Shekarau kan sauya sheka zuwa jam'iyyar APC
Asali: UGC

A yayin da shugaban jam'iyyar na kasa ke yabawa tsohon gwamnan jihar Kano dangane da sauyin shekar, ya kuma hikaito yadda ya bayar da muhimmiyar gudunmuwa wajen samar da kuma kafa jam'iyyar tun daga tsatson ta na tsohuwar jam'iyyar ANPP.

KARANTA KUMA: Wani 'Dalibi ya gamu da ajali a Makarantar horas da dakarun Soji, zargi ya fada zuciyar Iyayen sa

Oshiomhole ya kuma nemi gwamnan jihar Kano Ganduje, akan ya kulla alaka mai karfin gaske da tsohon gwamnan jihar domin jajircewa wajen kawo ci gaba da bunkasar kasar nan.

Jaridar ta Legit.ng ta ruwaito cewa, shugaban jam'iyyar da kuma gwamna Ganduje sun rinjayi sauyin shekar tsohon gwamnan jihar ta hanyar kwadaitar da shi wajen shige masa ta maye gurbin kujerar Sanatan kano ta Tsakiya, Rabi'u Kwankwaso a majalisar dattawa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel