Shekarau ya gana da dubban magoya bayansa, ya fadi dalilin fita daga PDP

Shekarau ya gana da dubban magoya bayansa, ya fadi dalilin fita daga PDP

- A jiya ne kafafen yada labarai a Najeriya suka wallafa rahotannin cewar tsohon gwamnan jihar Kano, Ibrahim Shekarau, ya canaja sheka daga PDP zuwa APC

- A yau, Asabar, ne shekarau ya gana da dubban magoya bayansa a jihar Kano domin shaida masu dalilinsa na ficewa daga jam’iyyar PDP

- Ana hasashen cewar jam’iyyar APC tayi alkawarin tsayar da Shekarau yam aye gurbin kujearar Sanatan Kano ta tsakiya, Rabi’u Musa Kwankwaso

Tsohon gwamnan jihar Kano, Malam Ibrahim Shekarau,ya bayyana cewar rashin adalcin da uwar jam’iyyar PDP ta nuna masa ne silar komawarsa jam’iyyar APC.

Shekarau ya bayyana hakan ne yayin gabatar da jawabi ga dubban magoya bayansa daga kananan hukumomin Kano 44 a wurin gangamin taron bikin karbarsa a jam’iyyar APC da aka yi a gidansa dake unguwar Mundubawa.

Shekarau ya gana da dubban magoya bayansa, ya fadi dalilin fita daga PDP
Shekarau ya gana da dubban magoya bayansa
Asali: Twitter

Shekarau ya gana da dubban magoya bayansa, ya fadi dalilin fita daga PDP
Shekarau ya gana da dubban magoya bayansa
Asali: Twitter

Tsohon gwamnan ya zargi shugabancin PDP na kasa da nuna rashin adalci a kan reshen jam’iyyar na jihar Kano.

DUBA WANNAN: Laifukan cin hanci da suka gagari EFCC

Shekarau ya ce ya bar PDP ne saboda shawarar da uwar jam’iyyar ta yanke na mika kashi 51% na shugabancinta a jihar Kano ga dan sanatan kano ta tsakiya kuma dan takarar shugaban kasa, Rabi’u Musa Kwankwaso.

Ana hasashen cewar jam’iyyar APC tayi alkawarin tsayar da Shekarau yam aye gurbin kujearar Sanatan Kano ta tsakiya, Rabi’u Musa Kwankwaso.

Shekarau ya gana da dubban magoya bayansa, ya fadi dalilin fita daga PDP
Shekarau ya gana da dubban magoya bayansa
Asali: Twitter

Shekarau ya gana da dubban magoya bayansa, ya fadi dalilin fita daga PDP
Shekarau ya gana da dubban magoya bayansa
Asali: Twitter

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng