Yadda 'yan Boko Haram suka yanka kaka na a gaban Ido na - Wani yaro mai shekaru 13

Yadda 'yan Boko Haram suka yanka kaka na a gaban Ido na - Wani yaro mai shekaru 13

- Wani kankanin yaro mai shekaru 13, Ibrahim Daniel , ya bayyana cewa 'yan Boko Haram ne suka kashe kakakansa

- Musa ya ce 'yan Boko Haram din sunyi amfani da wuka ne har sai da suka guntulle kan kakansa

- Ibrahim ya ce yana son ya shiga aikin soja idan ya girma saboda ya kare kansa daga 'yan Boko Haram

Mun samo daga arewa news cewa wata kafar yada labarai ta kai ziyara garin Gwoza da ke Borno domin hira da yaran da ake ceto daga hannun Boko Haram kai tsaye.

Manema labaran su tarar da yaran suna wasaninsu ne duk da cewa akwai zafin rana sosai amma basu damu da hakan ba inda suke kyalkyata dariya suna cudanya da junansu.

Yaran sun fito hutun karya kummalo ne a wata makarantan frimare na kudi da wata kungiyar sa kai 'Education Must Continue Inititative' da ke da hedkwata a Yola babban birnin jihar Adamawa ta kafa.

Ina kalo 'yan Boko Haram suka file kan kakana - Wani yaro da aka ceto
Ina kalo 'yan Boko Haram suka file kan kakana - Wani yaro da aka ceto
Asali: Facebook

Dukkan yaran da ke marantan 'yan gudun hijira ne da suka baro muhallinsu sakamakon hare-haren mayakan Boko Haram ke kaiwa a kauyukansu.

DUBA WANNAN: Dan takarar da ya kamata PDP ta tsayar muddin tana son kada Buhari - Makarfi

"Ina kalo 'yan Boko Haram suka file kan kakana.

"Sunyi amfani da wuka ne har sai da suka guntule masa kai," inji Ibrahim Daniel, wani yaro dan shekaru 13, dan asalin garin Gwoza.

Har a yanzu, wasu daga cikin 'yan ta'addan sukan buya a Gwoza. Boko Haram ta kwace garin na Gwoza a shekarar 2014, inda suka ayyana garin a matsayin hedkwatan daular da suka kafa.

Sun kafa bakar tutansu a wurare da dama a cikin garin, inda suke kashe duk wanda ya saba dokarsu a bainar jama'a daga baya su jefar da gawarsu a rijiya ko kududufi.

Sojin Najeriya sun fatataki 'yan Boko Haram daga garin Gwoza tun watanni tara da suka wuce amma har yanzu Daniel yana jin tsoron komawa garin.

"Baza kaso kaga 'yan Boko Haram ba, Ina son in zama soja saboda in rama dukkan abinda su kayi min," inji Daniel.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel