Hunkuyi ya shiga sahun masu takarar gwamna a jihar Kaduna

Hunkuyi ya shiga sahun masu takarar gwamna a jihar Kaduna

- Sanata mai wakiltan Kaduna ta Arewa a majalisar tarayya, Suleiman Hunkuyi ya sanar da niyarsa na takarar gwamna a jihar Kaduna

- Sanata Hunkuyi zaiyi takaran ne karkashin jam'iyyar PDP

- Hunkuyi ya ce ya shiga takarar ne saboda jama'an Kaduna suna bukatar wani da sauya akalan shugabanci a jihar

Rahoton da muka samu daga Daily Trust na cewa, Sanata Suleiman Uthman Hunkuyi, mai wakiltan Kaduna ta Arewa ya sanar da niyyarsa na tsayawa takarar gwamnan a zaben 2019 karkashin jam'iyyar PDP.

Sanatan da ya sauya sheka daga APC zuwa PDP ya yi wannan sanarwan ne a yau Juma'a a taron jin ra'ayi tare da shugabanin jam'iyyar PDP da masu ruwa da tsaki daga kananan hukumomi 11 a Unguwan Wakili da ke karamar hukumar Zangon Kataf.

Da duminsa: Hunkuyi ya fito takarar gwamna a jihar Kaduna
Da duminsa: Hunkuyi ya fito takarar gwamna a jihar Kaduna
Asali: Facebook

Sanata Hunkuyi ya dade yana sa-in-sa da gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna tun kafin ya baro jam'iyyar APC ya koma PDP.

DUBA WANNAN: An kama wani mutum da ya kira shugaban kasa biri

Wata sanarwa da ta fito daga bakin mai taimakawa sanatan a kafafen yada labarai, ta ce "lokaci ya yi da zamu kawar da wannan canjin a jihar Kaduna."

An sa ran kowanne lokaci daga yanzu, Sanatan zai sayi fam din takarar gwamnan a karkashin jam'iyyar PDP domin shiryawa zaben fitar da gwani a nan gaba.

Sanatan ya ce ya yanke shawarar yin takarar gwamnan ne saboda jama'a suna bukatar wani da zai sauya akalan shugabanci a jihar.

Sanarwan ta kuma ce shugabanin jam'iyyar PDP da masu ruwa da tsaki da suka hallarci taron sunyi alkawarin bawa Hunkuyi goyon baya domin cimma burinsa a jihar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel