Abin ala’ajabi: Hotunan tunkiyar da aka haifa da kafafuwa 5 da rabi

Abin ala’ajabi: Hotunan tunkiyar da aka haifa da kafafuwa 5 da rabi

Ikon Allah sai kallo, a kasar Netherland ne aka haifi wata yar tinkiya a da wani abin al’ajabi wanda ba’a saba ganin hakan ba, kai har ta kai ga uwar tinkiyar ta fatattaketa saboda abin mamakin da tazo da shi.

Jaridar Aminiya ta ruwaito an ita dai wannan tinkiya an haifeta ne da kafafuwa biyar da rabi, kuma tana nan a wani gidan gona dake unguwar Cornsay cikin karamar hukumar Durham dake tsibirin Texel.

KU KARANTA: Mutane miliyan 150 ke amfani da harshen Hausa wajen magana a fadin Duniya

Abin ala’ajabi: Hotunan tunkiyar da aka haifa da kafafuwa 5 da rabi
Tinkiya
Asali: Depositphotos

Sai dai duk da cewa uwar wannan tinkiya ta fatattaketa, toh amma ai dama masu iya magana sun ce bakin da Allah ya tsaga baya hana masa abinci, sai ga shi matar dake da wannan dabbobi ta rike wannan tinkiya kamar yarta, tana shayar da ita madara kamar yadda ake shayar da jarirai.

Wannan Mata mai suna Angie Jewitt ta bayyana cewa fatan shine Allah ya raya wannan tinkiya a yadda aka halicceta, don haka ne ma ta wareta daga cikin sauran tumakanta domin ta bada kyakkyawar kulawar da take bukata.

Abin ala’ajabi: Hotunan tunkiyar da aka haifa da kafafuwa 5 da rabi
Tinkiya
Asali: Depositphotos

Majiyar Legit.ng ta ruwaito ba kasafai ake samun irin wannan dabba ba, asali ma binciken masana halittar dabba ya nuna ana samun irin wannan ne a cikin haihuwar dabbobi miliyan daya, don kuwa kafafuwar wannan tinkiyar suna nan kamar kafafuwa hudu, sai dai rabin ne ke makale a gefen jikinta.

Uwargida Angie ta bayyana jin dadinta da lafiyar wannan tinkiya mai abin al’ajabi, inda tace a yanzu haka tana cikin koshin lafiya, haka zalika likitocin dabbobi sun ce tinkiyar bata bukatar ayi mata tiyata.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel