Mutane miliyan 150 ke amfani da harshen Hausa wajen magana a fadin Duniya

Mutane miliyan 150 ke amfani da harshen Hausa wajen magana a fadin Duniya

Sakamakon wani sabon bincike da cibiyar spectator index ta yi ya nuna harshen Hausa na daga cikin harsunan Duniya da suka fi samun karbuwa a tsakanin al’ummomin Duniya.

Jaridar Herald ta ruwaito harshen Hausa wanda aka fi amfani da shi a yankin Arewacin Najeriya ne harshen a goma sha daya a jerin mukamai na harsunan da jama’a suka fi amfani dasu.

KU KARANTA: Jigo a jam’iyyar PDP ya gamu da ajalinsa a hannun yan bindiga a jihar Adamawa

Majiyar Legit.ng ta ruwaito binciken cibiyar spectator ya bayyana cewar akwai masu amfan da harshen Hausa miliyan 150 a duk fadin Duniya, hakan ya nuna harshen Hausa ya zarce harshen Punjabi da miliyan biyu, kuma yayi ma harshen Jamusanci zarra da milian 21.

Haka zalika alkalumman da binciken ya fitar ya tabbatar da cewr harshen Hausa tayi ma abokiyar takararta a nahiyar Afirka, Swahili zarra da akalla mutane miliyan 47.

Sai dai bincike yace harshen mandarin ne harshe mafi yawan jama’an dake amfani da shi, wanda mafi yawancin masu amfani da wannan harshen sune al’ummar kasar China, akwai mutane biliyan daya da miliyan casa’in dake furta wannan harshen.

Ga jerin manyan harsunan na Duniya tare da adadin jama’an dake amfani da harsunan a adadin miliyoyi:

Mandarin miliyan 1090

Turanci miliyan 983

Hindustani miliyan 544

Spaniya miliyan 527

Larabci miliyan 422

Malay miliyan 281

Rasha miliyan 267

Bengali miliyan 261

Portuguese miliyan 229

Faransanci miliyan 229

Hausa miliyan 150

Punjabi miliyan 148

Jamusanci miliyan 129

Japanese miliyan 129

Parisanci miliyan 121

Swahili miliyan 107

Telugu miliyan 92

A wani labarin kuma a cikin makonni biyu da suka gabata ne aka yi bikin ranar Haura karo na hudu a shafukan yanar gizo, inda aka bukaci duk wani bahaushe ma’abocin kafafen sadarwar zamani da yayi amfani da harshen Hausa wajen rubuce rubucensa.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng