An cika kwana 1000 da Gwamnatin Najeriya ta cafke Zakzaky

An cika kwana 1000 da Gwamnatin Najeriya ta cafke Zakzaky

Mun samu labari cewa a yau dinnan ne Shugaban Kungiyar IMN ta Shi’a watau Ibrahim Yakub El-Zakzaky yayi kwanaki 1000 cur a garkame a hannun Gwamnatin Najeriya ba tare iznin Kotu ba.

An cika kwana 1000 da Gwamnatin Najeriya ta cafke Zakzaky
An shirya zanga-zanga a Abuja domi a saki Zakzaky
Asali: Twitter

Yau ‘Yan kungiyar Shi’a ta IMN ta ke shirin yin zanga-zanga na musamman domin nuna rashin jin dadin ta da damke Ibrahim Zakzaky da aka yi. Tun a Disamban 2015 ne Jami’an tsaro su kayi gaba da Shehin na Shi’a har yau.

Babban Kotun Tarayya ta bada iznin a saki babban Malamin da Iyalin sa, sai dai har yanzu Gwamnati tayi mursisi ta ki bin umarnin Kotun. Dama dai ana zargin Gwamnatin Buhari da sabawa umarnin Kotu yadda ta ga dama.

Wata Kungiya mai suna Concerned Nigerians ta shirya zanga-zangar da babu Musulmi babu Kirista domin nunawa Gwamnatin kasar rashin amincewan ta da garkame Ibrahim Zakzaky da ake cigaba da yi ba tare da bin ka’ida ba.

KU KARANTA: Oshimohole da Ganduje za su gana da Shekarau

Adeyanju Deji ya bayyana cewa yau za ayi wannan zanga-zanga da karfe 11:00 na safe a gaban Sakatariyar Ma’aiktar ilmi a tsakiyar babban Birnin Tarayya Abuja. Mabiya bayan addinin na Shi’a su na cigaba da kira saki Shehin na su.

Idan ba ku manta ba kwanan nan dai ‘Yan Shi’ar da dama sun shiga hannun Jami’an tsaro a lokacin da su ke zanga-zanga domin a saki babban Malamin na su da ya fi shekara 2 da rabi a tsare.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel