Buhari bashi da wata nagarta, tsantsagwaron yaudara ce - Lamido
- Tsohon gwamna jihar Jigawa, Sule Lamido, ya ce yaudara ce da karya ace wai Buhari ne kawai mai nagarta a Najeriya
- Lamido ya ce tun kafin Buhari akwai 'yan Najeriya da yawa masu nagarta kuma za'a samu wasu bayansu
- Lamido ya kuma yi ikirarin cewa Buhari baya girmama tsaffin shugabanin Najeriya masu nagarta
Tsohon Ministan harkokin kasashen waje kuma daya daga cikin masu neman tikitin takaran shugabancin kasa karkashin jam'iyyar PDP, Sule Lamido, ya ce akwai alamar tambaya a kan nagarta da kima da ake ikirarin Buhari na da shi.
Lamido ya yi wannan furucin ne a yayin da ya tafi ofishin PDP na babban birnin tarayya Abuja domin mayar da fam din takararsa a jiya Laraba, inda ya ce PDP za tayi nasara muddin aka bashi tikitin takarar.
A cewarsa, akwai 'yan Najeriya masu nagarta kafin Buhari kuma bayan shi za'a samu wasu masu nagartan, saboda haka, ba jam'iyyar APC ba ce ta kirkiri nagarta.
DUBA WANNAN: Wasu na hannun daman 'yan takaran shugabancin kasa 2 a PDP za su koma APC
Lamido ya yi nuni kan yadda taken Najeriya ya ambaci mazan jiya masu nagarta tun kafin Buhari. "Muna da Obafemi Awolowo, Ahmadu Bello, Nnamdi Azikwe, Aminu Kano da Tafawa Balewa kuma dukkansu masu nagarta ne amma ko sau daya Buhari bai taba jinjina musu ba.
"Duk inda ya tafi, kokari yake ya sauya tarihi domin ya nuna shi kadai ke da nagarta. Kafin Buhari akwai nagarta da gaskiya da rikon amana kuma zai tafi ya bar su. Buhari zai gushe ya bar Najeriya. saboda haka nagartarsa duk yaudara ce."
Da yake tsokaci kan yiwuwar samun nasarsa a zaben 2019 idan ya samu tikitin, Lamido ya ce juriya da dogewarsa ya banbanta shi da sauran masu neman tikitin saboda a cewarsa yana daga cikin wadanda suka zauna a PDP lokacin da jam'iyyar ta shiga cikin matsi da rigingimu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng