Ilimi ya tabbare a zamanin nan – Inji Malamin daya cika shekara 35 yana koyarwa

Ilimi ya tabbare a zamanin nan – Inji Malamin daya cika shekara 35 yana koyarwa

Wani limamin addinin kirista, kuma mataimakin shugaban sakandarin cibiyar horas da kananan fastoci na Emmanuel Alayande Junior Seminary Diocesan, Rabaran Olusegun Falana ya bayyana cewa abu ne mai kyau idan yara tun suna kanana suka fara fuskantar kalubale a rayuwa.

Jaridar Tribune ta ruwaito Falana yana kira ga iyaye da kamata yayi tun da wuri su fara koya ma yaransu dabarun fuskantar kalubale a rayuwa tun sun kanana, don da haka ne zasu iya tarar duk wani kalubale da zasu fuskanta idan sun girma

KU KARANTA: 2019: Kwankwaso ya tattauna da kungiyar kiristocin Najeriya game da takarar shugaban kasa

Ilimi ya tabbare a zamanin nan – Inji Malamin daya cika shekara 35 yana koyarwa
Falana
Asali: Depositphotos

Falana ya bada misalin kansa, inda yace da farko so yayi ya karanci ilimin likitanci, amma sai aka samu akasi sakamakon jarabwarsa bai cika ba, kuma bashi da kudi balle ya sake zana jarabawar, don haka mahaifinsa ya bashi shawarar ya fara koyar da kannensa karatu, a haka ya cigaba har ya samu zana jarabwar a shekarar 1977, kuma ya samu shiga jami’ar Legas.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Falana ya koka kan yadda jama’a suke bada gudunmuwa aka lalata sha’anin ilimi a dalilin rungumar cin hanci da rashawa a wajen jarabawa tare da tilasta ma yayansu fannin karatun da basa so, bugu da kari Falana ya koka kan samun yawaitar takardar karatun bogi.

Haka zalika Falana yayi kira ga gwamnati da masu makarantun kudi dasu dage wajen tattauna wa mutanen dake neman koyarwa a makarantunsu, ta hanyar yi musu tambayoyi, a haka zasu gane ko sun san abinda suke yi.

“Ya kamata iyaye su horas da yayansu, amma fa bai kamata su basu taimako ta wajen neman shiga makaranta ba, ta wajen neman karin maki don sakamakon jarabawa yayi kyau, babu yadda zaka tsallake kalubale a rayuwa, don haka ya kamata iyaye su kyale yaransu su fuskanci kalubale, kuma su koyar dasu dabarun magancesu.” Inji shi.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel