Jam’iyyar APC ta yi watsi da tsarin kato bayan kato a zaben fidda gwani

Jam’iyyar APC ta yi watsi da tsarin kato bayan kato a zaben fidda gwani

Uwar jam’iyyar APC a jihar Kaduna ta yi yanke shawarar yin fatali da tsarin fidda gwani na zaben kato bayan kato, inda ta bayyana burin yin amfani da zaben fidda da gwani ta hanyar yin amfani da wakilan jam’iyya.

Legit.ng ta ruwaito shugaban APC na jihar Kaduna, Emmanuel Jekada ne ya sanar da haka bayan kammala taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar a ranar Alhamis, 6 ga watan Satumba a garin Kaduna.

KU KARANTA: 2019: Kwankwaso ya tattauna da kungiyar kiristocin Najeriya game da takarar shugaban kasa

Shugaba Jekada ya bayyana cewa da dama daga cikin shuwagabannin jam’iyyar a Kaduna sun goyi bayan yin amfani da tsarin amfani da wakilan jam’iyya wajen gudanar da zaben fidda gwani a dukkanin mukamai banda na shugaban kasa.

“Duba da kalubalen tsaro, kayan aiki da kuma kokarin tabbatar da zaman lafiya a jihar Kaduna, yawancin yayan jam’iyyarmu sun goyi bayan yin amfani da wakilai wajen zabo yan takarar da zasu wakilci jam’iyyar APC a mukamai daban daban a zaben fidda gwani.

“Wannan shine gaskiyar abinda yawancin yayan jam’iyyarmu suka bukata, basu yarda da zaben kato bayan kato ba, wannan shine sakamakon zaman da muka yi a yau, don haka nan bada jimawa ba zamu mika rahotonmu ga uwar jam’iyya dake Abuja.” Inji shi.

Daga cikin wadanda suka halarci zaman akwai mataimakin gwamnan jihar Kaduna, mukaddashin gwamnan jihar, Barnabas Bala Bantex, Kaakakin majalisa, Aminu Abdullahi Shagali, yan majalisun tarayya, yan majalisun dokokin jiha da sauran masu ruwa da tsaki.

A wani labarin kuma dan majalisa mai wakiltar al'ummar Kaduna ta tsakiya, Sanata Shehu Sani ya caccaki manufar jam'iyyar APC ta jihar Kaduna na yin amfani da zaben wakilan jam'iyya.

Shehu Sani ya bayyana haka ne a yayin daya jagoranci wata kungiya ta yan takarkaru a inuwar jam'iyyar APC zuwa babban ofishin uwar jam'iyyar APC dake Abuja, inda ya nuna dacewar yin amfani da tsarin kato bayan kato wajen fidda dan takara.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel