Hakkin makwabtaka: Mutumin da yayi ma makwabcinsa dukan mutuwa ya fada komar Yansanda

Hakkin makwabtaka: Mutumin da yayi ma makwabcinsa dukan mutuwa ya fada komar Yansanda

Rundunar Yansandan jahar Jigawa ta sanar da kama wani mutumi da take zargi da yi ma makabcinsa dukan kawo wuka har sai da ya kashe shi, inji rahoton gidan talabijin na Channels.

Kaakakin rununar, ASP Audu Jinjiri ne ya sanar da haka a ranar Laraba 5 ga watan Satumba, inda yace bayan mutumin ya kashe makwabcinnasa, sai kuma ya jefar da gawar nasa a cikin rijiya.

KU KARANTA: Yaki da cin hanci da rashawa: An fatattaki mai horas da kungiyar kwallon kafa ta Najeriya

Legit.ng ta ruwaito Kaakaki Jinjiri yace zasu gurnfanar da wannan mutumi gaban Kotu da zarar sun kammala gudanar da bincike game da wannan laifi da ake tuhumarsa.

Idan za’a tuna a kwanakin baya ne rundunar Yansandan jihar Jigawa ta kama wani matashi daya kashe budurwarsa ta hanyar shake mata wuya har sai da tace ga garinku nan saboda ta ki yarda ta zubar da cikin da yayi mata.

A wani labarin kuma, akalla mutane bakwai ne suka mutu a sakamakon ambaliyan ruwa da ya mamaye karamar hukumar Ringim tare da barnata gidaje da gonakai guda dubu biyu.

Shugaban karamae hukumar, Abdulrashin lllah Ringim ne ya bayyana haka ga manema labaru a yayin ziyarar jajantawa da suka kai masa, inda yae yace damunar bana tazo da karfi sosai, don har inda basu taba samun matsalar ambaliyar ruwa a ba yaba sun gamu da matsalar a bana.

Illah yace akalla mutane dubu arba’in da biyar ne suka rasa gidajensu, inda yace wasu daga cikin mamatan sun mutu ne a yayin da suke kokarin neman mafaka, yayin da wasu kuma suka mutu a gidajensu.

Daga cikin abubuwan da aka yi asararsu akwai makarantu, masallatai, asibitoci, masallatai da amfanin noma na miliyoyin nairori, don haka yayi kira ha hukumar bada agajin gaggawa ta jahar Jigawa ta kai musu agaji.

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel