Kamfanin giya ya kai agaji makarantun jihar shari'a ta Kano, sun kuwa amsa

Kamfanin giya ya kai agaji makarantun jihar shari'a ta Kano, sun kuwa amsa

- Azuzuwa takwas da Dakin karatu kamfanin Maltina sukayi a kano

- Gwamna Abdullahi Ganduje ya jinjiinawa kamfanin

- Al'ummar Dorayi Babba ne suka bada filin don ginin

Kamfanin giya ya kai agaji makarantun jihar shari'a ta Kano, sun kuwa amsa
Kamfanin giya ya kai agaji makarantun jihar shari'a ta Kano, sun kuwa amsa
Asali: Facebook

Gwamnatin jihar kano ta kaddamar da azuzuwa takwas da Dakin karatu da kamfanin Maltina tayi a kwalejin fasaha dake gwale a birnin kano.

Gwamna Abdullahi Ganduje, wanda sakataren gwamnatin jihar, Alhaji Usman Alhaji, ya wakilta a bikin kaddamarwa da ya gudana a ranar juma'a, ya jinjiinawa kamfanin akan wannan aikin da sukayi.

Ganduje yayi kira ga yan Najeriya masu kumbar susa da kamfanonin hadaka da suyi koyi da wannan aikin, domin kawo cigaban bangaren ilimi.

DUBA WANNAN: Masu bukatar agaji sun kai 1m

Manajan Daraktan kamfanin, Mista Jordi Borrut yace wannan na daga cikin hobbasan da kamfanin yayi domin hada kai da Gwamnatin jihar gurin kawo cigaba a bangaren ilimi.

Sakataren Gwamnatin jihar, Alhaji Musa Alhaji ya jinjiinawa Al'ummar Dorayi Babba da suka bada fili kyauta don tallafawa tabbatar aikin.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel