Majalisar dinkin duniya tace kusan mutum miliyan daya ne basu samun agaji a Najeriya

Majalisar dinkin duniya tace kusan mutum miliyan daya ne basu samun agaji a Najeriya

- Kasashen turai sun gargadi UN cewa sama da mutane 800,000 ne aka datse daga tallafi a arewa maso gabas a Najeriya

- Rashin tallafin na iya jawo rasa rayukan mutanen arewa maso gabas

- Hakan yaci karo da abinda gwamnatin kasar ke fada

Majalisar dinkin duniya tace kusan mutum miliyan daya ne basu samun agaji a Najeriya
Majalisar dinkin duniya tace kusan mutum miliyan daya ne basu samun agaji a Najeriya
Asali: UGC

Kasashen turai sunyi gargadi ga UN cewa sama da mutane 800,000 ne aka datse daga tallafi, wanda kuma zai iya jawo rasa rayukansu a arewa maso gabas din Najeriya.

Hakan yaci karo da abinda gwamnatin kasar ke fadi, na samun saukin rikicin da ake a yankin.

Gwamnatin Najeriya tace a yanzu tallafin da bangaren arewa maso gabas na kasar take bukata bayan shafe sama da shekaru goma da hare haren Boko Haram, shine aiyukan cigaba a yankin.

DUBA WANNAN: Azumin kwana 40 ya hallaka shi

Amma a wasika zuwa daraktocin aiyukan gaggawa na UN da sauran cibiyoyin taimako, kungiyar hadin kan turai, Birtaniya da Jamus tace UN ta kasa bada tallafin gaggawa, wanda hakan zai iya kawo mutuwar kananan yara sakamakon yunwa.

Wasikar tace, mutane 823,000 ne basu da damar samun tallafi a jihar Borno, ta Najeriya. Inda harin yan ta'addan Boko Haram yafi shafa.

Kasashen turan sunyi kira ga Gwamnatin Najeriya da ta tsaya tsayin daka wajen ganin ta sauke hakkin ta na karewa da taimakon yan kasar ta.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel