Dan fashi ya tsunduma teku don kar a kama shi

Dan fashi ya tsunduma teku don kar a kama shi

- Wani dan fashi ya daka tsalle ya fada teku a Legas saboda kada 'yan sanda su kama shi

- Kungiyar sun shahara ne wajen daukan fasinjoji a mota sannan suyi musu fashi su jefar da su

- Dan fashin ya tsunduma cikin tekun dauke da dukkan kudade da wayoyin jama'a da suka kwace

A ranar Litinin ne wani matashi dan kungiyar 'yan fashi, ya tsunduma cikin teku da gadar Third Mainland a Legas saboda kada 'yan sanda su kama shi.

Matashin mai suna Junior ya fada cikin tekun ne misalin karfe 1 na rana kamar yadda sauran 'yan kungiyarsu suka fadi.

An gano cewa Junior da sauran 'yan kungiyar uku, Amos Williams, 21, Paul Olise, 37 da John Akinyemi sun yiwa wasu mutane hudu fashi ne a kusa da Ketu/Alepere a hanyar zuwa Oshodi.

Dan fashi ya tsunduma teku don kar a kama shi
Dan fashi ya tsunduma teku don kar a kama shi
Asali: Twitter

A maimakon su sauke fasinjojin da suka yiwa fashi a Oshodi, 'yan fashin sun garzaya dasu zuwa Iyana Oworo sannan suka fara jefar da su a kan titi daya bayan daya.

DUBA WANNAN: Mutane 5 na neman EFCC ta basu N49m da aka tsinta cikin buhu

Wani direba ya ga lokacin da aka turo daya daga cikin wadanda aka yiwa fashin daga motar kuma bayan ya tsaya ya taimaka masa, sai direban ya fara bin motar 'yan fashin amma da ya hango 'yan sandan SARS (RRS) a kan gada, sai ya tsaya.

Wanda aka yiwa fashin ya sanar da 'yan sandan SARS abinda ya faru dashi kuma daga nan suka fara bin 'yan fashin a baya amma kafin su kama 'yan fashin sai suka gane cewa su ake bi.

"Junior ya daka tsalle daga motar. Motocci biyu sun bige shi sannan ya daka tsalle ya fada cikin teku. 'Yan sanda kuma sun kama sauran mutane ukun," inji wata majiya.

Semiu ya shaidawa 'yan sanda cewa 'yan fashin sun kwace masa N500,000 da kuma wayoyin salularsa.

A yayin da yake gabatar da wanda ake zargi ga 'yan jarida a yau Laraba, Kwamishinan 'yan sanda, Imohimi Edgal, ya tabbatar da fakuwar lamarin inda ya ce 'yan sandan RRS da ke aikin sa ido a gadar Third Mainland ne suka damke 'yan fashin.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel