Kar ka damu Baba: ‘Yan Najeriya sun fara hada kudi don sayawa Buhari fam din takara

Kar ka damu Baba: ‘Yan Najeriya sun fara hada kudi don sayawa Buhari fam din takara

- Wata sabuwar matsala da yanzu haka ta saka ‘ya’yan jam’iyyar ta APC cikin damuwa ita ce ta tsadar kudin fom din takara

- Hatta Shugaba Buhari sai da ya yi korafi a kan tashin gwauron zabi da farashin fam din takara a CPC ya yi

- Sai dai wasu masoya shugaba Buhari sun ce kar ya damu da tsadar fam domin zasu hada kudi su saya masa

Karin kudin fam din kujeru a APC ya saka masu son yin takarar gwamnoni da majalisa a jam’iyyar guna-guni tare da kira ga kwamitin gudanarwa na jam’iyyar (NWC) da ya sake duba batun farashin fam din.

Wasu dake burin yin takara a APC sun aike da takardar korafi ga NWC a kan su rage farashin fam din da kuma kudin na-gani-ina-so da suka fitar tare da yin barazanar zasu shigar da karar jam’iyyar muddin ba ta gaggauta rage kudin fam din ba.

Hatta shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi korafi da tsadar kudin fam din takarar shugaban kasa da aka APC ta yanke masa farashi a kan miliyan N55m.

Kar ka damu Baba: ‘Yan Najeriya sun fara hada kudi don sayawa Buhari fam din takara
Tallafi wani daga cikin wadanda ke hada kudi don sayawa Buhari fam
Asali: Twitter

Sai dai wasu masoya shugaba Buhari sun ce kar ya damu da tsadar fam domin zasu hada kudi su saya masa.

Masu hada kudin, yawancinsu matasa, na daukan hoto na kudin da suka bayar tare da saka hoton a shafinsu na sada zumunta dake Tuwita.

DUBA WANNAN: 2019: Wasu matsaloli 2 sun fara sukurkuta APC

Ya zuwa yanzu babu masaniyar yadda ake tattara kudin da matasan ke ikirarin suna hadawa domin sayawa Buharin fam dinsa na takara.

APC ta ce masu son takarar gwamna zasu yanki fam a kan miliyan N22.5, masu takarar sanata zasu sayi nasu a kan miliyan N8.5m, majalisar wakilai a kan miliyan N3.8m, yayin da masu takarar majalisar dokokin jihohi zasu yanki nasu fam din a kan miliyan N1.1m.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel