APC ta Kano ya tabbatar da tsarin kato bayan kato a zaben fidda gwani

APC ta Kano ya tabbatar da tsarin kato bayan kato a zaben fidda gwani

Jam’iyyar APC reshen jahar Kano ta amince da gudanar da tsarin kato kato a zaben fidda gwani a tsakanin yan takarkaru dake neman darewa mukamai daban daban a jahar, inji rahoton jaridar Daily Nigerian.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito jam’iyyar ta bayyana haka ne a ranar Laraba, 5 ga watan Satumba bayan kammala taron shuwagabannin jam’iyyar tare da sauran masu ruwa da tsaki daya gudana a jahar.

KU KARANTA: Bankin Duniya za ta taimaka ma Najeriya da naira biliyan 216 don gamawa da Boko Haram

Cikin wata sanarwa da shugaban jam’iyyar Abdullahi Sunusi ya fitar bayan taron yace jam’iyyar ta yanke wannan shawarar gudanar da kato bayan kato a zaben fidda gwani na yan takarar shugaban kasa, gwamna, da sauran yan majalisu.

APC ta Kano ya tabbatar da tsarin kato bayan kato a zaben fidda gwani
Jam'iyyar APC
Asali: Depositphotos

Shugaba Abdullahi Sunusi ya bayyana cewa wannan mataki na zaben kato bayan kato zai kara ma jam’iyyar martaba a jahar Kano, tare da tsaftace hanyar fitar da dan takarar da jama’a ke so.

Haka zalika wannan mataki na jam’iyyar APC ya samu sahhalewar gwamnan jahar Kano Abdullahi Ganduje, Sanatocin jihar Kano guda biyu, Sanata Kabiru Gaya da Sanata Barau Jibrin, da yan majalisun tarayya guda 13 a karkashin shugabancin Ado Alhassan Doguwa.

Sauran masu fada aji a jam’iyyar da suka amince da wannan tsari sun hada da yan majalisun dokokin jahar Kano guda 33 a karkashin jagorancin kaakakin majalisar Kabiru Alhassan Rurum, shuwagabannin jam’iyyar APC guda 53.

Bugu da kari shuwagabannin kananan hukumomin jahar Kano su 44, da shuwagabannin APC a kananan hukumomi 44, da ma sakatarorinsu 44 sun amnince da gudanar da zaben kato bayan kato wajen fitar da yan takara.

Daga karshe shugaban jam’iyyar, Abdullahi Sunusi yace kato bayan kato zai baiwa yan jam’iyya kwarin gwiwa tare da tabbatar da adalci a zaben, haka zalika zai tabbatar da sahihanci da ingancin zaben.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags:
APC
Online view pixel