Karamin yaro dan shekara 15 ya cizge kansa da kansa bayan shan kaye a wasannin gyam

Karamin yaro dan shekara 15 ya cizge kansa da kansa bayan shan kaye a wasannin gyam

Wani karamin yaro mai shekaru goma sha biyar, Pavel Mateev ya kashe kansa sakamakon samun rashin sa’a a wani wasan gyam dayake bugawa a gidansu, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito wannan yaron yayi amfani ne da na’urar zarto wanda ake amfani da ita wajen yankan bishiya, inda ya kunnata a wuyarsa, har sai da tayi ajalinsa sanadiyyar mummunan rauni data ji masa.

KU KARANTA: Bankin Duniya za ta taimaka ma Najeriya da naira biliyan 216 don gamawa da Boko Haram

Rahotanni sun bayyana cewa Mateev ya shaku da wannan wasan gyam da mahaifiyarsa ta saya masa, wanda har ta kai ya kan kwashe awanni akan yana bugawa ba tare da ya gaji ba.

Gidan talabijin na gwamnatin kasar Rasha, NTV, ta bayyana cewa wannan yaro da mahaifiyarsa sun fito ne daga yankin Tomsk, kuma zuwa yanzu rundunar Yansandan kasar Rasha ta kaddamar da bincike akan lamarin.

A wani labarin kuma, hukumar kiwon lafiya ta duniya (World Health Organisation) tace mugun sabo da video game na janyo tabin hankali. WHO tace dabi'ar dai tana zama jiki ne a cikin watanni 12.

"Kafin a tabbatar mutum na da tabin hankalin, sai an gano cewa video game yana shiga cikin al'amuran mutum, iyali, karatu, aikin yi da kuma sauran abubuwa masu amfani na rayuwar Dan 'adam." Inji binciken na hukumar kula da lafiya ta majalisar dinkin duniya.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng