Bankin Duniya za ta taimaka ma Najeriya da naira biliyan 216 don gamawa da Boko Haram
Babban bankin duniya ta sanar da alkawarin taimaka ma yaki da Boko Haram da zambar kudi dala miliyan 600, tare da taimaka ma yan gudun hijira da rikicin ya shafa, inji rahoton kamfanin dillancin labaru, NAN.
Majiyar Legit.ng ta ruwaito bankin ta sanar da haka ne a yayin babban taron kasashen duniya akan yaki da Boko Haram dake gudana a birnin Berlin, babban birnin kasar Jamus tun daga ranar Litinin zuwa Talata 4 ga watan Satumba.
KU KARANTA: Fitaccen musulmin dan kwallon Duniya ya wanke bandakin masallaci a Ingila
Kasar Najeriya, Jamus, Norway da majalisa dinkin duniya ne suka shirya wannan taro na kwanaki uku don tattauna matsalar tsaro da kungiyar ta’addanci na Boko haram ta haifar, daya shafi nasarorin da aka samu da kuma kalubalen da ake fuskanta.
Baya ga babban bankin duniya, itama bankin cigaban Afirka da bankin Musulunci sun taimaka ma kasashen dake yankin tafkin Chadi da kudade da basussuka masu saukin ruwa.
Shugaban sashin kula da taimaka ma yan gudun hijira na majalisar dinkin duniya, Mark Lowcock ya bayyana godiyarsa ga bankunan da ma kasashen dake bada gudunmuwa wajen kawar da wannan matsala.
“Godiya ga bankin duniya daya taimaka ma yankin tafkin Chadi da kudin dala miliyan 600, haka zalika jinjina ga bankin cigaban Afirka daya bada kyautan kudi dala miliyan 35.65 ga yankin tafkin Chadi, da bashin dala miliyan57.3.” Inji Lowcock.
Mista Lowcock yace bankin Musulunci ma ya taimaka da bashin kudi dala miliyan 80, kasar Ireland ma ta taimaka da kyautan kudi yiro miliyan 7.3, Sweden ta bada pam miliyan 32, Netherland dala miliyan 12.1, Italiya dala miliyan 15 sai kuma kasar Poland da ta bada pam dubu 230.
Majiyar Legit.ng ta ruwaito an tara kudade da suka kai dala biliyan 2.2 a yayin wannan taro don taimakawa wajen yaki da Boko Haram tare da kulawa da yan gudun hijiar da rikciin ya daidaita.
Sauran kasashen da suka bada gudunmuwarsu a yayin wannan taro sun hada da mai masaukin baki Jamus da ta yi alkawarin taimakawa da yiro miliyan 265, Norway dala miliyan 125, Switzerland dala miliyan 20, Faransa yiro miliyan 131, Belgium yiro miliyan 45, da kasar Finland mai yiro miliyan 2.3.
Denmark ma ba’a barta a baya ba yayin da ta taimaka da dala miliyan 72.5, kasar Biryaniya ta bada pam miliyan 146, Canada dala miliyan 68, kungiyar kasashen tarayyar turai ta bada yiro miliyan 231.5, Luembourg yiro miliyan 40 da kuma Sifen da ta taimaka da yiro miliyan 3.2.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng