Duniya ta zo karshe: Matashi musulmi yayi garkuwa da mahaifinsa, ya kashe shi daga baya

Duniya ta zo karshe: Matashi musulmi yayi garkuwa da mahaifinsa, ya kashe shi daga baya

Runudunar Yansandan jihar Osun ta sanar da kama wani matashi mara Imani a ranar Talata, 4 ga watan Satumba wanda ake zarginsa da yin garkuwa da mahaifinsa tare da halaka shi, inji rahoton kamfanin dillancin labaru, NAN.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito sunan wannan matashi Isa Adamu mai shekaru 27, wanda ake zargi da hada wasu miyagun mutane masu satar mutane suka sace mahaifinsa mai shekaru 55, Ibrahim Adamu, tare da kashe maihaifin nasa bayan sun karbi kudin fansa.

KU KARANTA: Fitaccen musulmin dan kwallon Duniya ya wanke bandakin masallaci a Ingila

Kwamishinan Yansandan jahar, Fimihan Adeoye ne ya bayyana haka a lokacin da yake nuna ma manema labaru wannan matashi a shelkwatar Yansanda dake Osogbo, inda yace a ranar 27 ga watan Afrilu ne aka sace Adamu a gidansa dake Ede jihar Osun, inda aka yi awon gaba da shi a cikin motarsa.

Kwamishinan yace bayan sun samu rahoton faruwar lamarin, sun kama wani da ake zargi mai suna Jola-Anabi Saheed, inda aka gurfanar da shi a gaban Kotu, daga bisani kotun ta bada belinsa, daba nan kuma ya tsere ba’a sake ganinsa ba.

“Ganin haka yasa muka cigaba da gudanar da bincike wanda ta kai mu ga kama mutane uku dake da hannu cikin yin garkuwa da Malam Ibrahim Adamu, daga ciki har da dansa Isa, binciken ya nuna mana cewa dansa Isa ne ya dauki hayan mutanen domin su yi garkuwa da mahaifinsa.

“Saboda rashin Imani sai suka kashe Malam Ibrahim bayan sun karbi kudin fansa daga iyalansa na naira miliyan uku, sa’annan suka binne gawarsa a gefen wani rafi, inda a yanzu haka ruwa yayi gaba da gawar, kamar yadda suka tabbatar mana.” Inji kwamshina.

Kwamshinan ya kara da cewa yaron mamacin ya tabbatar ma yansanda cewa abokan aikinnasa sun yi alkawarin biyansa kudi naira dubu dari biyar (500,000) daga cikin miliyan uku da suka amsa, amma daga karshe sai suka bashi naira dubu arba’in da biyar.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel