Atiku ya fadi bakaken maganganu a kan Buhari

Atiku ya fadi bakaken maganganu a kan Buhari

- Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya bayyana tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan, a matsayin jarumi saboda karbar faduwa zabe da ya yi a 2015

- Atiku ya kira shugaban kasa Muhammadu da cewar mutum ne da giyar mulki ke bugarwa da kuma riko da ra’ayin rikau

- Kazalika, Atiku ya zargi Buhari da fakewa da siyasa domin cigaba da mulkin soja ta hanyar matsawa ‘yan jam’iyyar adawa da sunan yaki da cin hanci

A ranar Litinin ne tsohon shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya bayyana shugaba Buhari a matsayin mutumin dake cikin mayen giyan mulki tare da yin riko da ra’ayin rikau.

Yanzu muna fama da mulkin tsohon soja, mai ra’ayin rikau dake cikin mayen giyar mulki. Mun san ba zai bar mulki ta hanya mai sauki ba kamar yadda tsohon shugaban kasa Gooluck Jonathan ya karbi kayen da aka yi masa a 2015 ba,” in ji Atiku.

Atiku ya fadi bakaken maganganu a kan Buhari
Atiku Abubakar
Asali: UGC

Kazalika, Atiku ya yaba wa tsohon shugaban kasa Jonathan tare da bayyana shi a matsayin jarumi saboda karbar kayen da shugaba Buhari ya yi masa a zaben 2015.

DUBA WANNAN: Dan takarar gwamna a jihar Bukola ya fita daga PDP, ya koma APC

Sai dai wadannan kalamai na Atiku sun jawo masa raddi daga ‘yan Najeriya dake biye das hi shafinsa dake dandalin sada zumunta na Tuwita.

Wasu daga cikin masu mayar da raddi sun nuna fushinsu a kan maganganun da Atiku ya fada a kan shugaba Buhari tare da fadin cewar yana sukar shugaban kasa ne saboda ya takura wa mutanen da suka saci kudin gwamnati a baya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel