Jam’iyyar APC ta zama mafakar barayin yan siyasa - Secondus

Jam’iyyar APC ta zama mafakar barayin yan siyasa - Secondus

- Jam'iyyar PDP ta zargi barayin yan siyasa da kokarin ganin Buhari yayi tazarce

- Uche Secondus yace jam'iyyar APC ta zama mafakar barayin gwamnati

- Yace rashawa mafi muni shine magudin zabe da siyan kuri’u

Shugaban jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Uche Secondus yayi zargin cewa barayin yan siyasa na hada runduna domin dawo da Shugaba Muhammadu Buhari a 2019.

Da yake magana yayin kaddamar da kungiyar yakin neman zaben gwamnan jihar Osun da za’a gabatar a ranar 22 ga watan Satumba, Secondus yace jam’iyyar APC ta mayar da kanta mafakar barayi inda ya kara da cewa irin wadannan mutanen na samun kariya da kwanciyar hankali.

Shugaban PDP din yace rashawa mafi muni shine magudin zabe da siyan kuri’u .

Jam’iyyar APC ta zama mafakar barayin yan siyasa - Secondus
Jam’iyyar APC ta zama mafakar barayin yan siyasa - Secondus
Asali: Depositphotos

Yace a Osun, jam’iyyar adawa bazata lamunci lamarin day a faru a lokacin zaben gwamnan jihar Ekiti wadda aka gudanar a watan Yuli ba.

KU KARANTA KUMA: Hukumar kwastam sun kwace haramtattun kayayyaki na kimanin N50m

A nashi bangaren, Shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki wadda ya kasance shugaban kwamitin mutane 85 dake jagorantar yakin neman zabenna jihar Osun, ya kalubalanci Buhari da ya tsaya akan furucin da yayi a lokacin da shugabannin duniya biyu suka ziyarci kasar.

Shugaba Buhari yace zai tabbatar da an gudanar da zabe na gaskiya da amana.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel