Rikita-rikita: Fada ya kacame tsakanin Kwankwaso da Shekarau a Kano

Rikita-rikita: Fada ya kacame tsakanin Kwankwaso da Shekarau a Kano

- Fada ya kacame tsakanin Kwankwaso da Shekarau a Kano

- Fadan dai na da alaka ne da rushe shugabannin jam'iyyar PDP na jihar

- Shekarau da magoya bayan sa sunce bata sabuwa

Jam'iyyar adawa a jihar Kano ta Peoples Democratic Party (PDP) ta yi fatali tare da kin amincewa da matsayar da uwar jam'iyyar ta kasa ta dauka na sauke dukkan shugabannin zartarwar jam'iyyar daga Abuja.

Rikita-rikita: Fada ya kacame tsakanin Kwankwaso da Shekarau a Kano
Rikita-rikita: Fada ya kacame tsakanin Kwankwaso da Shekarau a Kano
Asali: Depositphotos

KU KARANTA: Wani gwamna a Najeriya ya roki Buhari ya yafewa barayi

Daya daga cikin jogogin jam'iyyar a jihar Kano mai suna Sarki Labaran da kuma ke zaman daya daga cikin na hannun daman tsohon gwamnan jihar Malam Ibrahim Shekarau ne ya sanar wa da wasu magoya bayan jam'iyyar da suka taru a hedikwatar jihar.

Legit.ng ta samu cewa shima jagoran jagoran jam'iyyar a jihar Malam Ibrahim Shekarau a cikin wani sako da ya fitar wa magoya bayan jam'iyyar, ya nuna rashin amincewar sa da matakin da babbar jam'iyyar ta dauka.

Masu sharhi dai na ganin wannan tamkar wata 'yar manuniya ce da ke tabbatar da zargin mutane na cewa manyan 'yan siyasar a jihar ba zasu taba zama a cikin inuwa daya ba.

A wani labarin kuma, Jami'an 'yan sandan Najeriya shiyyar jihar Delta dake a yankin kudu maso kudancin kasar nan sun tabbatar da sace wani babban malamin addinin kirista ajihar mai suna Rabaran Fada Christopher Ogaga a garin Oviri-Okpe dake a karamar hukumar Okpe.

Kamar dai yadda muka samu, Kwamishinan 'yan sandan jihar Alhaji Muhammad Mustafa shine ya sanar wa da manema labarai hakan a garin Warri, daya daga cikin manyan garuruwan dake a jihar.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel