Nayi nadamar gaza yiwa PDP wani muhimmin aiki a 2003 – Atiku

Nayi nadamar gaza yiwa PDP wani muhimmin aiki a 2003 – Atiku

A jiya, Litinin, ne Alhaji Atiku Abubakar, ya bayyana cewar yayi nadamar rashin taimakon jam’iyyar PDP wajen lashe zabuka a jihar Legas a shekarar 2003.

Mai neman PDP ta tsayar da shi takarar shugaban kasa a zaben 2019, Alhaji Atiku Abubakar, ya bayyana wa ‘yan jam’iyyar a jihar Legas babbar nadamar sa.

Kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) ya rawaito Atiku na fadawa ‘yan majiyar PDP, yayin ganawa dasu a jihar Legas, cewar ya yi nadamar gazawarsa wajen taimakon jam’iyyar ta kafa gwamnati a jihar Legas a shekarar 2003.

Atiku ya yi waiwayen baya a kan yadda tsohon shugaban kasa Obasanjo ya dora masa alhakin tabbatar da jam’iyyar PDP tayi nasara a zabukan shekarar 2003 a jihohin yankin kudu maso yamma da jam’iyyar AD keda karfi a wancan lokacin.

Nayi nadamar gaza yiwa PDP wani muhimmin aiki a 2003 – Atiku
Atiku Abubakar
Asali: Depositphotos

Tsohon shugaban kasar ya ce a lokacin sai da ya yi nasar kawowa jam’iyyar PDP dukkan jihohin yankin kudu maso yamma in banda jihar Legas.

A cewar Atiku, ya kyale jihar Legas ne saboda kyakykyawar dangantaka dake tsakaninsa da tsohon gwamnan jihar Legas a wancan lokacin, Bola Tinubu.

Bayan na nemi Obasanjo ya damka min ragamar yakin neman zabe a jihohin kudu maso yamma kuma ya amince da hakan, nayi nasara a dukkan jihohin yankin in ban da jiharv Legas.

DUBA WANNAN: Jan aiki: PDP ta kafa kwamitin kwace mulki daga hannun APC a karkashin Saraki

“Na kyale Legas ne a wancan lokacin saboda alakar dake tsakanina da tsohon gwamnan jihar, Bola Tinubu, a wancan lokacin.

“Na kyalewa Tinubu Legas ne saboda yadda muka yi gwagwarmayar siyasa tare a SDP da PDM. Amma duk da haka nayi nadamar rashin karbe Legas a wancan lokacin,” a cewar Atiku.

Kazalika, Atiku, ya nemi afuwar ‘yan jam’iyyar ta PDP tare da shaida masu cewar tuni ya yi nadamar barin jihar Legasb da ya yi a hannun Tinubu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel