Buhari ya ki saka hannu a kan wata doka da majalisa ta sake aika masa a karo na uku

Buhari ya ki saka hannu a kan wata doka da majalisa ta sake aika masa a karo na uku

- Wannan shine karo na uku da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ki rattaba hannu a kan dokar yiwa jadawalin zabe kwaskwarima

- Mai taimakawa shugaba Buhari a bangaren harkokin da suka shafi majalisar dattijai, Ita Enang, ya ce rashin gamsuwa da hujjojin majalisar ne ya saka shugaban kasa kin amincewa da dokar

- Majalisar dattijai ta kafe a kan sai an yiwa jadawalin zabukan zabe garambawul, wani kudiri da fadar shugaban kasa ke ganin akwai son rai a cikinsa

A karo na uku, shugaban kasa Muahammadu Buhari ya ki saka hannu a kan dokar yiwa jadawalin gudanar da zabukan Najeriya garambawul.

Mai taimakawa shugaba Buhari a bangaren harkokin majalisar dattijai, Ita Enang, ya shaidawa manema labarai cewar tuni shugaban kasa ya aikewa majalisun kasa, a cikin wata wasika mai dauke da kwanan watan ranar 30 ga watan Agusta, dalilinsa na kin amincewa da dokar.

Buhari ya ki saka hannu a kan wata doka da majalisa ta sake aika masa a karo na uku
Buhari ya ki saka hannu a kan wata doka da majalisa ta sake aika masa a karo na uku
Asali: Depositphotos

A cewar Enang, shugaba Buhari ya ki saka hannu kan dokar ne saboda rashin gamsuwar sa da wasu sassa na kudirin a yiwa jadawalin zabukan garambawul.

DUBA WANNAN: Aiki ja: PDP ta kafa kwamitin mutane 22 karkashin jagorancin Saraki don kayar da APC

Enang ya kara da cewar shugaba Buhari har shugabannin majalisa ya gayyata domin neman Karin haske a kan dalilin yiwa jadawalin zaben garambawul amma basu ba shi bayanin da zai gamsar da shi ba.

An dade ana tataburza tsakanin majalisa da shugaba Buhari a kan canja fasalin jadawalin zabuka da wasu dokokin zabe. Fadar shugaban kasa na zargin majalisa da yunkurin canja dokokin domin biyan bukatar kansu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel