Jami’in soja ya soki wani dan makaranta saboda bashi a Lagas (hoto)

Jami’in soja ya soki wani dan makaranta saboda bashi a Lagas (hoto)

Yan uwani wani matashi dalibin makarantar Lagos State Polytechnic, Abraham Enebeli, sun bukaci bi masu hakkinsu bayan wani soja ya soke shi.

Rahotanni sun kawo cewa wani jami’in soja na sashin Ojo soki Abraham a yankin Ijegun a ranar Asabar, 1 ga watan Satumba.

An tattaro cewa jami’in sojan mai suna Daniel Martins ya fasa kwalba sannan ya soki Abraham a wuya lokacin da wani sabani ya shiga tsakaninsu.

Dan uwan Abraham, Paul Enebeli ya bayyana cewa wani Chukwudi ne yayo hayan Martins.

Jami’in soja ya soki wani dan makaranta saboda bashi a Lagas (hoto)
Jami’in soja ya soki wani dan makaranta saboda bashi a Lagas
Asali: UGC

Paul yace: “Matsalan ya fara ne a farkon watan Agusta lokacin da Abraham yaci bashin kimanin N150,000 daga hannun Chukwudi.

“Abraham ya bayyana cewa wasu mutane sun damfare shi; amma sai Chukwudi ya je ya kwaso sojoji shida gidansa.

KU KARANTA KUMA: Ministan shari’a ya bukaci kotu da tayi watsi da karar da aka shigar kan tsige Saraki

“Sun yiwa dan uwana dukan tsiya, sun jiwa mahaifiyata rauni sannan suka yi yunkurin tafiya da daya daga cikin kanne na. Wasu mutane suka hana su. Sunyi barazanar ci gaba da zuwa har sai dan uwana ya biya kudin.

“An shiga yarjejeniya tsakanin Abraham, sojoji da kuma Chukwudi cewa tunda sun jiwa mutane da dama rauni akan lamarin dawo da kudinb, baza’a biya cikakken kudin ba. Suka yarda kan cewa dan uwana zai biya N85,000.

“Don haka, daya daga cikin sojojin ya ci gaba da tozarta dan uwana. A ranar Asabar sojan na a kana babur tare da wani abokinsa da ya san yayana.

“Dan uwana suka gaisa da abokin nasa. Sai sojan ya kira dan uwan nawa, amma yaki amsa shi. Hakan ya tunzura shi. Sai ya sauka daga kan babur dinsa ya ture dan uwan nawa.

“Sai cacan baki mai zafi ya shiga tsakaninsu kawai sai sojan ya dauki kwalba ya fasa ya soki yayana a wuyansa. A take yah aye babur dinsa ya bar wajen.”

Lokacin da aka tuntubi Chukwudi ya karyata cewan ya tura sojan wajen Abraham, inda ya kara da cewa kudin na jami’in sojan ne.

Kakakin sojin sashi na 81, Laftanal Kanal Olaolu Daudu yayi alkawarin yin bincike akan lamarin tare da daukar matakin day a kamata.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel