Baki har kunne: Yadda wasu Chanisawa suka kayatar da Buhari a kasar China (Bidiyo)

Baki har kunne: Yadda wasu Chanisawa suka kayatar da Buhari a kasar China (Bidiyo)

Shifimdar fuska ta fi ta tabarma, kamar yadda masu iya magana suke cewa game da bakunta, haka zalika al’adar karrama baki dadadden al’ada ne tsakanin al’adu da dama dake fadin Duniya, hakan ne ta tabbata ga shugaban kasa Muhammadu Buhari.

A ranar juma’a, 31 ga watan Agusta ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya halarci wani muhimmin taro na hadin kai tsakanin kasashen nahiyar Afirka da kasar China dake gudana a kasar ta China.

KU KARANTA: PDP: Bafarawa ya yi watsi da duk wani tayin sulhu da sauran yan takarar shugaban kasa

A yayin wannan ziyara ta shugaban kasa Muhammadu Buhari, gwamnatin kasar China ta yi masa babbar karamci, tare da girmamawa da kuma mutuntawa, da haka ne ta aiko da wata tawagar yan asalin kasar China dake jin harshen Hausa da Fillanci don su kayatar da Buhari.

Wadannan yan kasar China sun gabatar da rawa da wake wake da harshen fiilanci, wanda hakan ya baiwa mahalarta taron da kuma shugaba Buhari kansa, kamar yadda ma'abocin Facebook Buhari Sallau ya daura hotunan.

Bugu da kari shugaba Buhari ya aika ma yan adawarsa muhimmin sako daga kasar China, inda yace baya tsoron shiga takara matukar hukumar zabe mai zaman kanta, INEC, zata gudanar da zaben gaskiya da gaskiya.

Buhari ya bayyana haka ne a ranar Lahadi, 2 ga watan Satumba inda yace shine dan siyasan da yafi cin moriyar zaben gaskiya da gaskiya, don haka ba zai ji tsoron fafatawa a zaben gaskiya da gaskiya ba.

Daga karshe Buhari ya bayyana cewa zai tabbatar da hukumar INEC ta gudanar da zaben da yafi na shekarar 2015 adalci, haka zalika yace ya zama wajibi INEC da hukumar Yansanda su mutunta muradun yan Najeriya.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel