Adadin sojojin da Boko Haram suka kashe ya karu

Adadin sojojin da Boko Haram suka kashe ya karu

- A jiya, Asabar, ne mayakan kungiyar Boko Haram suka kai hari wani sansanin soji a jihar Borno

- Ana zargin cewar mayakan sun kashe manyan sojoji biyu da kananan sojoji 46

- Hukumar sojin Najeriya ta musanta rahotannin kai harin tare da musanta adadin wadanda suka mutu

Wani rahoto da jaridar Premium Times ta rawaito ya ce an samu karuwar sojoji 17 da suka rasa ransu a sakamakon harin da mayakan kungiyar Boko Haram suka kai masu.

A ranar Alhamis ne kafafen yada labarai suka rawaito cewar a kalla sojoji 46 ne suka rasa ransu yayin da suke kokarin kare harin da mayakan kungiyar Boko Haram suka kai sansanin sojojin.

Yanzu haka an sake gano gawar wani babban soja da wasu sojojin 16 yayin da kungiyar agaji ta isa sansanin da aka kai harin domin kiyasin asarar rayukan da aka yi.

Adadin sojojin da Boko Haram suka kashe ya karu
Sojojin Najeriya
Asali: Depositphotos

Jaridar Premium Times ta bayyana cewar majiyarta ta sanar da ita cewar mayakan kungiyar Boko Haram sun kai hari a sansanin sojojin Najeriya dake kauyen Zari mai iyaka da jamhuriyar Nijar ta gabashin jihar Borno.

Yanzu haka an mika gawar sojojin 17 da aka gano zuwa Maiduguri, cibiyar yaki da aiyukan ta'addanci na kungiyar Boko Haram, kamar yadda majiyar Premium Times ta rawaito.

DUBA WANNAN: Dandalin Kannywood: Ali Nuhu ya kara lashe wata babbar kyauta

Duk da hukumar sojin Najeriya ta yarda da rahotannin kai harin, ta bayyana cewar dakarunta ne suka kashe mayakan Boko Haram masu yawa.

Kanal Onyema Nwachukwu, kakakin rundunar soji ta Ofireshon Lafiya Dole, ya bayyana cewar rahoton adadin sojojin da suka mutu bai isa teburin sa ba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng