Daya daga cikin dan takarar shugaban kasa a PDP ya aurar da dansa, kalli hotuna
- Tsohon shugaban riko na PDP, Sanata Ahmed Makarfi ya aurar da dansa
- An daura auren Faisal Ahmed Mohd Makarfi, ne a yau a garin Kaduna
- Jiga-jigan jam'iyyar PDP na yanzu da wadanda suka sauka daga mulki sun hallarci daurin auren
Mun samo cewa a yau Asabar 1 ga watan Satumba ne aka daura auren dan tsohon shugaban shugaban riko na PDP kuma daya daga cikin masu neman takaran shugabancinsa kasa karkashin inuwar jam'iyyar, Sanata Ahmed Makarfi.
Kamar yadda wani ma'abocin amfani da shafin sada zumunta, Usman Umar Showay ya wallafa, an daura auren Faisal Ahmed Mohd Makarfi ne a garin Kaduna.

Asali: Facebook
DUBA WANNAN: Da duminsa: Wasu 'yan majalisar APC 3 sun fita daga jam'iyyar

Asali: Facebook
Jiga-jigan jam'iyyar PDP da dama sun hallara wurin dauren auren cikinsu har da tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, gwamna Dankwambo, tsohon gwamnan Kaduna, Ramalan Yero, tsohon gwamnan jihar Katsina, Barrister Shehu Shema.

Asali: Facebook
Sauran sun hada da tsohon gwamnan Benue, Gabriel Suswan, tsohon gwamnan Jigawa, Sule Lamido, Hon. Abdul Dokan Tagwai da sauran manyan baki.

Asali: Facebook

Asali: Facebook

Asali: Facebook
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng