2019: Dan takarar gwamna a PDP ya koma APC saboda Buhari

2019: Dan takarar gwamna a PDP ya koma APC saboda Buhari

- Michael Olawole Cole, mai neman PDP ta tsayar da shi takarar gwamna ya fita daga jam'iyyar

- Ya bayyana cewar ya shiga APC ne bayan gamsuwa da ya yi da salon mulkin shugaba Buhari da gwamna Ambode na jihar Legas

- Olawole ya ce bai shiga APC ba sai bayan gamsuwa da ya yi da irin yadda suke tafiyar da al'amuran gwamnati

Mai neman takarar gwamnan Legas a karkashin PDP, Dakta Olawole Cole, ya fita daga jam'iyyar bayan ya bayyana gamsuwarsa da salon mulkin shugaba Buhari da gwamna Ambode na jihar Legas.

A wata ganawa da ya yi da manema labarai a yau, Asabar, Olawole, ya sanar da cewar ya koma jam'iyyar APC kuma tuni har ya yanki katin shaida a mazabar sa ta 'A' Onigbongbo dake Ikeja a jihar Legas.

2019: Dan takarar gwamna a PDP ya koma APC saboda Buhari
2019: Dan takarar gwamna a PDP ya koma APC saboda Buhari
Asali: Depositphotos

Olawole ya bayyana cewar ya yanke shawarar komawa jam'iyyar APC ne bayan yabawa da irin salon tafiyar da harkokin gwamnati da shugaba Buhari ke yi a tarayya da kuma na gwamna Ambode a matakin jiha.

KU KARANTA: Da duminsa: Balarabe Musa ya ajiye shugabancin jam'iyyar PRP

"Bayan dadewa a PDP tare da yi mata takarar gwamna a jihar Legas a zaben 2007, zan iya cewa tabbas akwai banbanci tsakanin jam'iyyun biyu.

"Daga salon mulkin shugaba Buhari a tarayya da na gwamna Ambode a jihar Legas da irin tsaftataccen mulkin APC, zaka san cewar duk mai son cigaba zai goyi bayan jam'iyyar.

"Na rike mukamin kwamishinan kudi da kuma na aiyuka a jihar Legas, sannan na kasance mamba a PDP na tsawon shekaru 4. Amma duk da hakan na fi gamsuwa da manufofin APC da salon mulkin ta", a cewar Olawole.

Olawole ya kara da cewar tabbas akwai 'yan kura-kurai a yadda wasu abubuwan ke gudana a gwamnati tare da bayyana cewar duk da hakan niyya da manufofin kayutatawa jama'a da kasa na jam'iyyar APC sun fi na PDP kyau.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel