Sauran kiris zalamar mulkin Saraki ta ruguza APC - Oshiomhole

Sauran kiris zalamar mulkin Saraki ta ruguza APC - Oshiomhole

- Ciyaman din APC, Adams Ohiomhole ya ce ficewar Bukola Saraki daga APC alkhairi ne

- Oshiomhole ya ce kadan ya rage da bakin burin Saraki ya tartwatsa jam'iyyar APC

- Dama Oshiomhole ya sha fadin cewa son kai ne ba kishin kasa yasa Saraki ke tayar da kayan baya a APC ba

Ciyaman na kasa na jam'iyyar APC, Adams Oshiomhole ya ce sayan tikitin takarar shugabancin kasa da shugaban majalisa, Bukola Saraki, ya yi a jam'iyyar PDP ya nuna karara cewa neman mulki ne ke gabansa ba kishin kasa ba.

Oshiomhole ya ce hadamar Saraki ta kusa ruguza jam'iyyar APC, inda ya kara da cewa ficewar Saraki daga jam'iyyar shine yafi zama alkhairi.

Sauran kiris zalamar mulkin Saraki ta ruguza APC - Oshiomhole
Sauran kiris zalamar mulkin Saraki ta ruguza APC - Oshiomhole
Asali: UGC

A taron da Oshiomhole ya yi da shugabanin APC a jihar Kwara, ya ce kadamar da takarar shugabancin kasa da Saraki ya yi ya fitar dashi daga zargi inda ya shawarci 'ya'yan jam'iyyar su ajiye son zuciya su yi aiki domin kawo karshen babakeren da Saraki ke yi a jihar.

DUBA WANNAN: Kotu ta hana mikawa Kwankwaso PDP a Kano

A jawabin da ya yi ta bakin sakataren yada labaransa, Simon Ebegbulem, Oshiomhole ya ce 'yan siyasa irinsu su Saraki basu da wata akida illa karkata bangaren da za su samu 'maiko' saboda basu kishin 'yan Najeriya.

Ya kara da cewa har yanzu 'yan Najeriya basu manta da irin wahalhalun da jam'iyyar PDP ta jefa su ciki ba, hakan yasa 'yan Najeriya ba za su waiwayi jam'iyyar ta PDP ba.

"Wani basarake a Najeriya ya ce 'yan Najeriya ba za su yi gagawan yafewa jam'iyyar PDP laifukansu ba. Ko da kana son ka yafewa mutum, sai kaga ya canja halayensa.

"Sun lalata mana tattalin arziki, sun lalata mana tsarin zabe, sune suka koyawa 'yan najeriya magudin zabe. Sune suka kawo siyasar a mutu ko ayi rai." inji Oshiomhole.

DUBA WANNAN: Mun gaji da bakin ikon da Saraki ke nuna mana - Mutanen jihar Kwara

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel