Gwamnatin Tarayya da Gwamnoni da Kananan Hukumomi sun raba Biliyan 714

Gwamnatin Tarayya da Gwamnoni da Kananan Hukumomi sun raba Biliyan 714

Mun samu labari cewa wannan watan Najeriya ta samu sama da Naira Biliyan 714. Abin da aka samu dai yayi kasa idan aka kamanta da kudin da aka samu a watan jiya.

Gwamnatin Tarayya da Gwamnoni da Kananan Hukumomi sun raba Biliyan 714
Ministar kudin Najeriya Kemi Adeosun a wajen wani taro
Asali: Depositphotos

Labari ya zo mana daga Jaridar Vanguard cewa Gwamnatin Najeriya ta samu Biliyan 714.18 wanda aka raba tsakanin Gwamnatin Tarayya da Jihohi da kuma Kananan Hukumomin Kasar nan a matsayin kason watan Agusta.

Abin da Najeriya ta samu a wannan watan bai kai ainihin abin da Kasar ta samu a watan jiya ba. A watan da ya gabata, Gwamnatin Najeriya ta samu kusan da Naira Biliyan 820. Ministar kudin Kasar Kemi Adeosun ta bayyana wannan.

KU KARANTA: Matar Gwamnan Bauchi za ta raba mutane da shaye-shaye

Kudin da Najeriya ta samu ya fito ne daga gangunan man fetur da kasar ta saida. Akwai kuma Biliyoyin da aka samu ta bangaren arzikin sauran ma’danai da kuma haraji da sauran su. Ministar ce ta bayyanawa menama labarai hakan.

A cikin kason da aka samu an karawa Jihohin da ke da arzikin man fetur Biliyan 44.96 a matsayin ladan rijiyoyin man fetur din da su ke da shi. A ka’ida dama ana ba Jihohin da ke da man fetur kashi 13% na abin da aka samu.

Gwamnatin Tarayya ce dai ta dauki kusan Biliyan 270 daga cikin wannan kudi, Gwamnoni kuma sun raba Naira Biliyan 136.5 yayin da Kananan Hukumomi su ka samu fiye da Naira Biliyan 100.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Online view pixel