2019: Sule Lamido ya kuma yin kaca-kaca da Jam'iyyar APC

2019: Sule Lamido ya kuma yin kaca-kaca da Jam'iyyar APC

Daya daga cikin ‘Yan takarar Jam’yyar PDP Sule Lamido yana cigaba da kai ziyara Jihohin kasar nan domin ganin ya samu goyon baya a zaben fitar da gwani na Jam’iyyar PDP da za ayi nan gaba.

2019: Sule Lamido ya kuma yin kaca-kaca da Jam'iyyar APC
Alhaji Sule Lamido ya kai ziyara Jihar Benuwai domin kamfen din 2019
Asali: UGC

Daily Trust ta rahoto Tsohon Gwamnan Jigawa Sule Lamido yayi kaca-kaca da APC inda yace Jam’iyyar ba ta da aikin yi sai batawa ‘Yan adawar ta suna. Lamido ya kuma nuna cewa babu abin da APC ta sa a gaba sai karyar masifa a Najeriya.

Tsohon Gwamnan ya bayyana wannan ne lokacin da ya gana da Gwamnan Jihar Benuwe Samuel Ortom da wasu manyan PDP a Jihar. A cewar tsohon Gwamnan na Jigawa, APC ba ta da aiki sai kokarin shafawa PDP baki da kashi a kasar.

‘Dan takarar na Shugaban kasa ya nuna cewa APC ta yaudari jama’a ne ta dare mulki inda yace idan ya samu mulki za ayi wa kasar nan sauyin fasali kamar yadda mutane da dama su ke kira, yana kuma mai neman ganin an samu hadin kai.

KU KARANTA: 'Dan takarar PDP ya sha alwashin ceto ‘Yan Najeriya daga kangi

Sule Lamido ya kuma koka da yadda kashe-kashe ya zama ruwan dare a Najeriya inda yace ya kamata Jama’a su yi kokari wajen ganin sun zabi PDP a 2019 domin maganin sha’anin tsaro da kuma kawo zaman lafiya mai dorewa a kasar.

Lamido wanda ya cika shekaru 70 a makon nan dama yace Shugaban kasa Muhammadu Buhari bai iya daukar adawar ‘Yan siyasa saboda abin da ya koya a gidan Soja yana kuma mai neman ganin an marawa duk wanda PDP ta tsaida baya.

Alhaji Sule Lamido ya kai ziyara Jihar Benuwai ne domin samun goyon bayan manyan PDP inda ya gana da Mataimakin Gwamnan Jihar. Kafin na dai Lamido ya ziyarci jagororin PDP a Jihar Bauchi da kuma Jos duk a cikin 'yan kwanakin nan.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel