Yaki da ta’addanci: Masarautar a Zamfara zata fara yiwa kauyukan Fulani maja

Yaki da ta’addanci: Masarautar a Zamfara zata fara yiwa kauyukan Fulani maja

- Masarautar Anka a jihar Zamfara ta bayyana cewar zata fara hade kauyukan Fulani wuri guda domin rage yawaitar hare-haren da ake samu a yankin

- Sarkin Anka, Attahiru Ahmad, ya ce masarautar ta yanke wannan shawara ne domin nuna goyon bayanta ga kokarin gwamnatin tarayya na kawo zaman lafiya a yankin

- Jihar Zamfara ta dade tana fama da hare-haren ‘yan bindiga da suka yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama

Masarautar Anka a jihar Zamfara ta bayyana cewar zata hade kauyukan Fulani dake tarwatse a sassan masarautar domin magance yawaitar hare-hare da ake kaiwa mazauna rugar Fulani da kananan kauyuka.

Sarkin Anka, Attahiru Ahmad, ya ce masarautar ta yanke wannan shawara ne domin taimakawa gwamnatin tarayya a kokarinta na tabbatar da zaman lafiya a jihar.

Yaki da ta’addanci: Gwamnatin Zamfara zata fara yiwa kauyukan Fulani maja
Abdulaziz Yari, Yemi Osinbajo da Buhari
Asali: Depositphotos

Abinda muke son yi kwatankwacin shirin gwamnatin tarayya ne na kirkirar burtalin kiyo ga makiyaya. Muna son rage yawan Fulani dake zaune a kananun kauyuka da suke a tarwatse a wannan masarauta. Yin hakan zai kawo sauki wajen magance yawaitar hare-hare da ke kaiwa kauyukan da kuma bayar da dammar gano daga inda ‘yan bindigar dake kai hare-haren ke zuwa,” a cewar Mai Martaba Ahmad, yayin wata gana da manema labarai yau, Alhamis, a garin Anka.

DUBA WANNAN: Harin da wasu giwaye 3 suka kai a jihar Kebbi ya saka jama'a cikin zullumi

Mai martaba Ahmad ya kara da cewa, “mun dade muna kokarin fadakar da Fulanin a kan amfani hade kauyukan tare da nusar da su cewar hakan zai bawa gwamnati dammar kawo masu aiyukan cigaba da zasu inganta rayuwar su.”

Jihar Zamfara ta dade tana fama da tashe-tashen hankula daga harin ‘yan bindiga day a yi sanadiyyar mutane da dama.

Yanzu haka gwamnatin tarayya ta aike da rundunar sojoji karkashin atisayen Ofireshon Dirar Mikiya domin kawar da ‘yan bindigar dake kai hare-hare a sassan jihar ta Zamfara.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel