Ba zan bar PDP ba kuma ina tare da duk wanda Jam’iyya ta tsaida – Dankwambo

Ba zan bar PDP ba kuma ina tare da duk wanda Jam’iyya ta tsaida – Dankwambo

Daya daga cikin manyan ‘Yan takarar Shugaban kasa a Jam’iyyar adawa ta PDP kuma Gwamnan Jihar Gombe Ibrahim Dankwambo yayi magana game da rade-radin cewa zai bar Jam’iyyar PDP.

Ba zan bar PDP ba kuma ina tare da duk wanda Jam’iyya ta tsaida – Dankwambo
Dankwambo za su marawa duk wanda PDP ta ba tuta baya
Asali: UGC

Darekta Janar na taya Dankwambo yakin neman zaben Shugaban kasa a 2019 watau Farfesa Terhemba Shija yace Gwamnan bai da niyyar ficewa daga Jam’iyyar PDP. Terhemba Shija yace babu dalilin da zai sa Dankwambo barin Jam'iyyar PDP.

Sarkin yakin takarar Gwamna Ibrahim Hassan Dankwambo ya bayyana cewa a 2015 lokacin da Jam’iyyar APC ta karbe Jihohin Arewa, Gwamna Dankwambo bai yi watsi da PDP ba don haka babu dalilin da zai sa ya tsere daga Jam’iyyar PDP.

KU KARANTA: Buhari ba zai samu kuri'a miliyan 12 a 2019 ba - Turaki

Ibrahim Hassan Dankwambo ya nuna cewa ko da bai samu lashe tikitin Jam’iyyar PDP, zai marawa duk wanda Jam’iyyar ta tsaida baya a zaben Shugaban kasa a 2019. Gwamnan yace PDP na da Shugabannin da za su iya mulkin kasar nan a 2019.

Ana tunani Gwamnan na Gombe yana da karfi a Yankin Arewa maso Gabas kuma yana cikin Gwamnonin da su ka fi karfi a PDP. Wasu manyan ‘Yan takarar PDP irin Sule Lamido dai sun ce ko wa Jam’iyyar ta tsaida za a mara masa baya.

Tsohon Gwamnan Jigawa Sule Lamido ya kai ziyara Jihar Bauchi da Jos lokacin da ya ziyarci manyan Jam’iyyar PDP a Yankin. Lamido ya nemi mutanen Jihar Bauchi su marawa duk wanda PDP ta tsaida takarar Shugaban kasa baya a zaben 2019.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel