Kwankwaso yayi alkawarin inganta harkar ilmi idan ya samu mulki
Mun samu labari cewa ‘Dan takarar Shugaban kasa a Jam’iyyar PDP Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso yayi alkawarin inganta harkar ilmi a kasar nan idan har ya zama Shugaban Kasa a 2019.

Asali: Twitter
Tsohon Gwamnan Kano Rabiu Kwankwaso wanda ya fito takarar Shugaban kasa na zaben 2019 a karkashin Jam’iyyar PDP yace idan ya samu mulkin kasar nan zai yi kokarin ganin an babbako da harkar ilmi a Najeriya.
Kwankwaso ya kaddamar da shirin sa na tsayawa takara ne yau a babban Birnin Tarayya Abuja a Unguwar Jabi. Kwankwaso yace da ilmin Boko ne za ayi maganin banbance-banbancen da ake samu tsakanin jama’ar kasar nan.
KU KARANTA: Shugaba Buhari da APC sun ji tsoron Kwankwaso – Inji CUPP
Sanatan na Kano ta tsakiya Kwankwaso a wajen taron kaddamar da shirin takarar Shugaban kasa yake cewa idan ya samu mulkin Najeriya a karkashin PDP, kowa zai yi karatu kyauta tun daga matakin Firamare har zuwa Jami’a.
‘Dan takarar ya nuna cewa da ilmi ne za a maida kowa ya zama daidai a Kasar sannan kuma ayi maganin rashin hadin kai da zama lafiya da ake samu. A lokacin yana Gwamna a Jihar Kano, Kwankwaso ya inganta harkar ilmi.
Dazu kun ji cewa Gwamnatin Buhari ta jawowa kan ta bakin-ciki na hana Kwankwaso kaddamar da shirin takarar Shugaban Kasa. Jiya ne aka sanar da cewa za a hana Kwankwaso taro a farfajiyar
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng