Ku yi ma mayakan Boko Haram ruwan bala’I ba sassautawa – Babban kwamanda ga Sojoji

Ku yi ma mayakan Boko Haram ruwan bala’I ba sassautawa – Babban kwamanda ga Sojoji

Babban kwamandan rundunar Sojin Najeriya ta 7 dake jibge a garin Maiduguri na jihar Borno, Birgediya janar Bulama Biu ya umarci dakarun Sojin Najeriya da kada su kuskura su nuna Imani ga mayakan Boko Haram, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Majiyar Legit.ng ta ruwaiyto Birgediya Bulama ya bayyana haka ne a yayin daya kai ziyara ga wasu Sojoji da aka girke a garin Delwa dake cikin karamar hukumae Konduga, inda yayi kira garesu da suyi amfani da makamansu wajen karskashe yan Boko Haram.

KU KARANTA: Sunnah leka gidan kowa: kungiyar Izala ta bude ofis a birnin Makkah

Kaakakin rundunar, Texas Chukwu ya sanar da ziyarar da Biu ya kai ma Sojojin, inda yace Biu ya jinjina ma kokarin da Sojojin ke nunawa a yaki da yan ta’adda, sa’annan yayi kira garesu dasu taimaki junansu wajen ganin an cimma manufar da aka sa a gaba.

Daga cikin wadanda suka raka Kwamandan akwai Kanal Emmanuel Oyewole, KanalOluremi Obolo da kuma Kanal Babatunde Alaya, da sauran manyan shuwagabannin hafsoshin Soja dake rundunar.

A wani labarin kuma, rundunar Sojan kasa ta dauki alwashin hukunta duk wani sojan da ya nuna rashin da’a, ladabi da biyayya a yayin gudanar da aikinsa.

Babban kwamandan rundunar Soja dake yaki da Boko Haram, Manjo janar Abbah Dikko ne ya sanar da haka a ranar lahadin data gabata. Dikko yana magana ne game da wasu Sojoji da suka yi bore a kwanakin baya suka dinga harba bindiga a iska akan an turasu wani yankin jihar Borno don yaki da Boko Haram.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel