Mulkin Buhari ya raba kan 'yan Najeriya, ya jefa su cikin mawuyacin hali - Lamido

Mulkin Buhari ya raba kan 'yan Najeriya, ya jefa su cikin mawuyacin hali - Lamido

Tsohon gwamnan jihar Jigawa kuma mai neman takarar shugabancin kasa karkashin inuwar jam'iyyar PDP, Sule Lamido ya cacaki gwamnatin shugaba Buhari inda ya ce ta haifar da talauci da yunwa tare da raban kan al'ummar Najeriya.

Dan takarar shugabancin kasa karkashin jam'iiyyar PDP, Sule Lamido ya ce mulkin shugaba Muhammadu Buhari ta jefa dimbin 'yan Najeriya cikin yunwa da mawuyacin halin rayuwa.

Lamido ya yi wannan furucin ne a jiya Talata a garin Bauchi yayin da ya ke ganawa da deleget da magoya bayan jam'iyyar PDP sa jihar ta Bauchi. Ya kuma ce gwamnatin jam'iyyar APC ta raba kan 'yan Najeriya mababanta addini da kabila.

Mulkin Buhari ya rabawa kawunnan 'yan Najeriya, ya jefa su cikin yunwa - Lamido
Mulkin Buhari ya rabawa kawunnan 'yan Najeriya, ya jefa su cikin yunwa - Lamido
Asali: Facebook

A cewarsa Lamido, gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari tana zaban 'yan adawa ne kawai a lokacin da ke yaki da rashawa.

DUBA WANNAN: Kotu tayi fatali da bukatar dakatar da tsige Saraki

Ga kalamansa: "Idan kana jam'iyyar PDP, za su ce kai barawo ne, Idan kuma kana APC, ka zama waliyyi, wanne irin adalci ne wannan.

"Gwamna Ortom ya shafe shekaru uku yana mulki a jihar Benue, yana ficewa daga jam'iyyar APC sai EFCC ta fara gudanar da bincike a kanshi.

"Mun san cewa jam'iyyar APC na kare masu laifin rashawa da ke goyon bayan ta.

"Shugaba baya yiwa mutanensa barazana, yana mu'amulantarsu ne da adalc, tausayi da jin kai ba wai barazanar jefa su a gidan yari ba."

Lamido ya yi kira da deleget din jihar Bauchi su zabe shi a matsayin dan takarar shugabancin kasa na jam'iyyar PDP kuma su shirya jure barazana da gwamnatin APC za tayi musu a yunkurinsu na takarar zabe.

Ya ce muddin su kayi hakuri kuma suka jure duk abinda zai biyo baya, jam'iyyar PDP za ta lashe zaben shugabancin kasa a shekarar 2019 da sauran kujerun zaben.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel