Wani babban basarake ya gargadi ‘yan siyasa a kan bashi toshin kudi

Wani babban basarake ya gargadi ‘yan siyasa a kan bashi toshin kudi

Sarkin garin Warri ta jihar Delta, Olu Ogiame Ikenwoli, ya ce bashi da bukatar kudi ko abun hannun ‘yan siyasa tare da bayyana cewar ‘yan siyasar ne ke bukatar ya saka masu albarka.

Mai martaba Ogiame ya bayyana hakan ne a jiya, Talata, a fadar sa yayin karbar bakuncin Irone Rita Begho, mai neman takarar kujerar sanatan jihar Delta ta kudu a karkashin jam’iyyar APC.

Bayan ya yabi ‘yar takara Begho tare da nuna gamsuwa da gogewar ta, sarki Ogiame ya bukaci ‘ya’yan kabilar Itsekiri da su dawo gida domin inganta yankinsu.

Wani babban basarake ya gargadi ‘yan siyasa a kan bashi toshin kudi
Tsohon gwamnan jihar Delta Uduaghan yayin bude wani aiki
Asali: Facebook

A wani labarin na Legit.ng kun ji cewar tsagerun yankin Neja-Delta, karkashin hadakar kungiyoyin dake fafutikar neman 'yancin yankin, sun yi barazanar komawa kai hare-hare matukar gwamnatin tarayya ta ki amincewa da yiwa kundin tsarin mulkin kasa garambawul.

DUBA WANNAN: 2019: Cibiyar Turai ta fitar da sakamakon zaben gwaji da jin ra'ayin jama'a da ba zai yiwa PDP dadi ba

A wani jawabin da shugaban hadaddiyar kungiyar, Mista John Duku, ya saka wa hannu kuma aka raba ga manema labarai ranar Asabar a garin Uyo dake jihar Akwa Ibom, tsagerun sun ce yin barazanar ya zama dole ganin yadda gwamnatin jam'iyyar APC ke gudanar da salon mulkinta.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel