Magoya bayan Kwankwaso sunyi hatsari a hanyarsu ta zuwa Abuja

Magoya bayan Kwankwaso sunyi hatsari a hanyarsu ta zuwa Abuja

- Wasu daga cikin magoya bayan Sanata Rabiu Musa Kwankwaso sunyi hatsarin mota

- Sunyi hatsarin ne a hanyarsu ta zuwa taron kaddamar da takarar shugabancin kasa da Kwankwaso zai yi a Abuja

- Da yawa daga cikinsu sun jikkata kuma ana tsamanin akwai wadanda suka rasu sakamakon hatsarin

Mun samu cewa wasu magoya bayan Sanata Rabiu Musa Kwankwaso sunyi hatsari a hanyarsu a kan hayarsu ta zuwa taron kaddamar da takarar shugabancin kasa da ake gudanarwa a yau Laraba a babban birnin tarayya Abuja.

Magoya bayan Kwankwaso sunyi hatsari a hanyarsu ta zuwa Abuja
Magoya bayan Kwankwaso sunyi hatsari a hanyarsu ta zuwa Abuja
Asali: Twitter

Fasinjoji da yawa sun samu munnanan raunuka kuma ana kyautata zaton wasu sun rasa rayyukansu.

DUBA WANNAN: An gano wani korarren dan sanda cikin masu fashi da makami da aka cafke

Sai dai wasu daga cikin magoya bayan Kwankwaso tuni sun isa babban birnin tarayya Abuja lafiya inda tsohon gwamnan ke kaddamar da aniyarsa ta tsayawa takarar zaben shugabancin kasa karkashin jam'iyyar PDP.

A jiya, tsohon gwamnan na jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso ya yi ikirarin cewa gwamnatin tarayya na kokarin kawo masa cikas wajen kaddamar da takarar nasa da aka shirya yi a farfajiyar taro na Eagle square a ranar 29 ga watan Augustan 2018.

Kwankwaso ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da ta fito daga bakin kungiyar yakin neman zabensa (Kwankwaso Campaign Organisation) a jiya Talata 28 ga watan Augusta.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel