Buhari ya lashe zaben 2019 ya gama – Dan majalisa

Buhari ya lashe zaben 2019 ya gama – Dan majalisa

Wani mamba a majalisar dokokin jihar Nasarawa, Mista Murtala Sodangi ya amince da tsarin zaben fidda gwani kai tsaye wato shugaban jam’iyya da masu ruwa da tsaki na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) su zabi wanda zai tsayawa jam’iyyar takara a zabukan 2019.

Sodangi mai wakiltan mazabar Nasarawa ta tsakiya ya nuna goyon bayansa a ranar Talata, 28 ga watan Agusta a Nasarawa yayinda yake amsa tambayoyi daga manema labarai a yankin karamar hukunar Nsarawa dake jihar.

Jam’iyyar mai mulki ta sanar da shirin amfani da zaben fidda gwani kai tsaye wajen zabar yan takaranta na zabukan 2019.

Buhari ya lashe zaben 2019 ya gama – Dan majalisa
Buhari ya lashe zaben 2019 ya gama – Dan majalisa
Asali: Twitter

Jam’yyar ta gwada zaben fidda gwani na kai tsayen a lokacin zaben gwamnan jihar Osun na wanda zai tsaya mata.

A cewar Sodangi hakan zai ba mambobin APC damar da zasu zabi dan takarar da ransu ke so.

Sodangi yayi kira ga ‘yan Najeriya da ba Shugaban kasa Muhammadu Buhari goyon baya wajen yakar cin hanci da rashawa domin ci gaban kasar.

Ya bayyana Buhari a matsayin shugaba mai amana kuma mai yakar cin hanci da rashawa, don haka yana bukatar goyon baya don cimma nasara.

Ya kara da cewa, Buharimutum ne mai martaba, mara zamba kuma cewa In shaa Allah shine zai yi nasara a zaben 2019 saboda martabobinsa da babu mai iya kayar dashi.

KU KARANTA KUMA: Oshiomhole ya dauki gagarumin hukunci akan gwamnonin da basu yi abun azo a gani ba ta hanyar hana su yin tazarce

A halin da ake ciki, mambobin kwamitin koli na jam'iyya mai mulki sun amince da sabon tsarin fitar da gwani na 'yan takarar su a dukkan matakai a zaben gama gari na shekarar 2019 dake a tafe

Majiyar ta mu ta Daily Trust har ila-yau ta samu cewa wannan maganar dai ta tabbata ne a daren jiya lokacin da mambobin kwamitin da suka hada da Shugaban kasa Muhammadu Buhari, mataimakin sa da dai sauran jiga-jigan jam'iyyar suka gana.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel