Takarar shugaban kasa: Kwankwaso ya sanar da sabon dandalin da zai kaddamar da takararsa a Abuja

Takarar shugaban kasa: Kwankwaso ya sanar da sabon dandalin da zai kaddamar da takararsa a Abuja

Duk da hana shi yin amfani da dandalin Eagles square dake babban birnin tarayya Abuja don kaddamar da takararsa ta shugaban kasa a zaben shekarar 2019, tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso bai yi kasa a gwiwa ba.

Legit.ng ta ruwaito a ranar Talata, 28 ga watan Agusta ne dai manajan dandalin Eagles, Usman Raji ya aika ma kwamitin yakin neman zaben Kwankwaso cewa basu yarda su gudanar da gangamin a dandalin ba.

KU KARANTA: Katin zabe: Gwamnatin jahar Zamfara ta sanar da hutun gamagari a ranar Juma’a

Cikin wasikar da ya aika, manaja Raji yace: “sakamakon ranar Laraba rana ce ta aiki, don haka taro kamar wannan na siyasa zai takura ma ma’aikata gwamnati dake aiki a sakatariya gwamnatin tarayya, wanda take gab da dandalin.”

Sai dai jaridar Premium Times ta ruwaito mai magana da yawun Kwankwaso, Hajiya Binta Sipikin tana cewa sun samu wani sabon wurin da zasu gudanar da gangamin kaddamar da takarar Kwankwaso.

“Gangamin taron kaddamar da takarar shugaban kasa ta Sanata Rabiu Kwankwaso zai gudana ne a ranar Laraba 28 ga watan Agusta a Otal din Chida dake unguwar Utako a Abuja.” Inji ta.

A kwanakin baya ne tsohon gwamnan jihar Kano, Rabiu Kwankwaso ya sauya sheka daga jam’iyyar APC zuwa PDP, sa’annan ya gargadi jam’iyyar PDP da ta tabbata ta mika takarar shugaban kasa ga yanin Arewa maso yamma matukar tana son samun nasara a zaben 2019.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Online view pixel