2019: Cibiyar Turai ta fitar da sakamakon zaben gwaji da jin ra'ayi da ba zai yiwa PDP dadi ba

2019: Cibiyar Turai ta fitar da sakamakon zaben gwaji da jin ra'ayi da ba zai yiwa PDP dadi ba

Wani sakamakon zaben gwaji da jin ra’ayin jama’a da wata cibiyar Turai, Zeus Polls, ta gudanar ya nuna cewar jam’iyyar APC zata yi nasara a zaben 2019 tare da lashe kujerun gwamna fiye da wadanda take da su a yanzu.

Kamfanin Dillancin labarai na kasa (NAN) ya rawaito cewar cibiyar Zeus ta gudanar da wani bincike day a yi has ashen nasarar gwamna Willie Obiano a zaben gwamnan jihar Anambra da kuma Kayode Fayemi a zaben gwamnan jihar Ekiti.

Cibiyar Zeus, mai shelkwata a birnin Berlin na kasar Jamus, ta sanar da sakamakon zaben gwajin ne a yau, Talata, a cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai a Legas mai dauke da sa hannun jami’inta mai kula da gudanar da zaben gwaji da jin ra’ayin mutane, Tanko Suleiman.

Sakamakon zaben gwajin ya bayyana cewar duk da gunagunin da wasu ‘yan Najeriya ke yi a kan gwamnatin APC hakan ba zai hana ta samun nasarar lashe Karin wasu kujerun gwamna a zaben 2019 ba.

2019: An fitar da wani sakamakon jin ra’ayin mutane a Turai da PDP ba zata ji dadinsa ba
Buhari
Asali: Twitter

Cibiyar Zeus ta bayyana cewar daga cikin kuri’ar jin ra’ayi da ta gudanar a Kaduna, kasha 51% na jama’ar jihar sun nuna sha’awar sun a sake zaben gwamna Nasir El-Rufa’i na jam’iyyar APC kamar yadda mutane kaso 65% a Legas suka nuna sha’awar su ta sake zaben gwamna Ambode na APC.

A sakamakon zaben gwaji da aka gudanar a jihar Ribas da PDP ke mulki, kasha 65% na jama’a sun nuna basa son gwamnan jihar, Nyesom Wike, ya kara samun nasara a zaben 2019. Kazalika kaso 47% na jama’ar jihar sun nuna sha’awar sun a zaben dan takarar gwamnan a APC, Tonye Princewill.

DUBA WANNAN: Allah ya aiko Buhari ya ceci Najeriya - Gwamnan APC

A jihar Kano, kaso 65% na masu kada kuri’a sun bayyana cewar ba zasu sake zaben gwamnan jihar, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ba. Kaso 60% kuwa cewa suka yi zasu kada kuri’ar su ne ga duk dan takarar da tsohon gwamna Rabi,u Musa Kwankwaso ya goyawa baya.

Cibiyar ta kara da cewar ya zuwa yanzu bat a gama tattara kuri’u da ra’ayin masu zabe a kan wanda zasu zaba ya zama shugaban kasa ba a zaben 2019 tare da daukan alkawarin cewar nan ba da daewa ba zata saki sakamakon zaben gwanji a kan takarar shugaban kasa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Online view pixel