Yadda matasa suka halaka wani direban gada gada daya kade wata yarinya har lahira

Yadda matasa suka halaka wani direban gada gada daya kade wata yarinya har lahira

Fusatattun matasa sun sun lakada ma wani dalibin kwalejin kimiyya da fasaha dake garin Ede na jihar Osun, Fisayo Olorunfemi dukan kawo wuka, wanda yayi ajalinsa sakamakon tukin gada gada da yayi.

Legit.ng ta ruwaito wani shaidan gani da ido yana cewa Fisayo yana cikin wata mota ne kirar camry mai lamba AAA 463 DV a lokacin da ya buge wani dan achaba da fasinjar dake kai, inda nan take fasinjar mai suna Islamat Bello ta fadi matacciya.

KU KARANTA: Wuta ta cinye kananan yara 2 yan gida daya a wata mummunar gobara a Delta

Mutuwar wannan yarinya ne ya harzuka matasan yankin, wanda suka sauke fushinsu akan wannan dalibi har sai da yace ga garinku nan, kamar yadda kamishinan Yansandan jihar Fimihan Adeoye ya tabbatar.

Kwamishinan yace: “Na yi mamakin yadda mutane ke daukan doka a hannunsu, kaga yanzu sun kashe dalibin a banza, tunda dai mutuwarsa ba zata dawo da yarinyar ba, gaskiya bai kamata mutane suna irin wannan dabia irin na jahilai ba.”

Kaakakin rundunar Yansandan jihar, Folashade Odor ya tabbatar da mutuwar dalibin, inda yace tuni suka mika gawarwakin mutanen biyu zuwa dakin ajiyan gawarwaki dake babban asibitin Ede, haka zalika motar dalibin da babur din suna ofishin Yansanda.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel